Ko Real Madrid za ta iya lashe Gasar Zakarun Turai bana?
Shin ko Real Madrid za ta iya ɗaukar Gasar Zakarun Turai karo na 16 a bana?

A jiya Juma’a ce aka fitar da jadawalin zagayen ’yan 16 na Gasar Zakarun Turai ta bana a birnin Nyon.
Hukumar Ƙwallon Ƙafar Turai, UEFA, ta tsara yadda zagayen na ‘yan 16 da zagayen dab da na kusa da na ƙarshe da zagayen dab da ƙarshe da kuma zagayen ƙarshe za su kasance.
Za a kece raini ne a karawar farko ta zagayen ’yan 16 a ranakun 4 da 5 na watan Maris, inda za a yi karon-batta a karawa ta biyu bayan mako guda.
Mai riƙe da kambun gasar Real Madrid za ta kara da abokiyar hamayyarta na birni Atletico Madrid a maimaicin fafatawar ƙarshe na shekarun 2014 da 2016, waɗanda dukkaninsu Los Blancos ce ta samu galaba.
Liverpool za ta kece raini da takwararta Paris Saint-Germain a ɗaya daga cikin fafatawar da za su ɗauki hankali.
Bayern Munich za ta haɗu da abokiyar hamayyarta ta kasar Jamus Bayer Leverkusen, yayin da Arsenal za ta kara da PSV Eindhoven sannan Inter Milan za ta tunkari Feyenoord.
Barcelona za ta barje gumi da Benfica yayin da aston villa za ta hadu da Brugge, ita kuwa Borussia Dortmund za ta hadu da kungiyar Lille ta kasar Faransa.
Madrid wadda ta shiga cikin sahun masu neman gurbin zuwa zagayen ’yan 16 a kakar bana, ta yi waje rod da Manchester City wajen cimma wannan nasara.
Real Madrid ta sake doke Manchester City da ci 3 da 1 a filin wasa na Bernabeu, jimilla 6-2 a karawar da suka yi kashi biyu — gida da waje.
Madrid ta ce karɓi baƙuncin Manchester City a wasan karawa ta biyu bayan doke ta a gida (Etihad) da ci 3 da 2.
Ko a bara dai Real Madrid ce ta lashe gasar karo na 15 kuma mafi bajinta la’akari da cewa mataki ne da ba a taɓa samun wata ƙungiya ta yi makamancinsa ba a tarihi.
A karawar ƙarshe da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Borussia Dortmundta Jamus a filin wasa na Wembley, Real Madrid ta lallasa Jamusawan da ci 2-0.
Godiya ga ɗan wasan bayan Real Madrid, Dani Carvajal wanda shi ne ya yi kukan kura ya fara zura wa Dortmund ƙwallon farko a mintuna na 74 yayin da ɗan wasa Vinicius Junior shi ma ya gwada sa’arsa ya zura wa ƙungiyar ƙwallon ƙafar Jamus ɗin ƙwallo ta biyu a yayin da ake mintuna 83 da fara wasan.