Ko sakamakon Taron kasa zai haifar wa kasar nan da mai ido?
A makon jiya ne Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya karbi gundarin shawarwarin da mahalarta Taron kasa suka cimma bayan kammala taron wanda aka kwashe kimanin wata biyar ana gudanarwa. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko sakamakon taron zai haifar wa kasar nan da da mai ido kuwa? Ga ra’ayoyin wasu jama’a kamar yadda […]
A makon jiya ne Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya karbi gundarin shawarwarin da mahalarta Taron kasa suka cimma bayan kammala taron wanda aka kwashe kimanin wata biyar ana gudanarwa. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko sakamakon taron zai haifar wa kasar nan da da mai ido kuwa? Ga ra’ayoyin wasu jama’a kamar yadda wakilanmu suka zanta da su:
Babu amfanin da taron zai kawo – Alhaji Yahya Kutunga
Alhaji Yahya Kutunga: “Ina ganin babu alamar sakamakon zaman taron zai yi wa kasa baki daya amfani domin an fi mayar da hankali a wajen tattaunawa a kan abubuwan da za su raba kasa ne fiye da wadanda za su dinke ta. Misali wakilan taron da suka fito daga sashe daya da shugaban kasa wato, shiyyar Kudu-maso-Kudu, mai arzikin man fetur, sun mayar da hankali wajen tattauna batun rabon arzikin kasa da suke so shiyyar tasu ta mamaye kason fiye tsoka da sauran shiyyoyin kasar nan. Saboda haka nake ganin an barnatar da kudi ne kawai domin ruruta kabilanci da kyamar juna a tsakanin al’ummar Najeriya amma ba domin amfaninmu a nan gaba ba.”