Ko sakamakon Taron kasa zai haifar wa kasar nan da mai ido? 1

A makon jiya ne Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya karbi gundarin shawarwarin da mahalarta Taron kasa suka cimma bayan kammala taron wanda aka kwashe kimanin wata biyar ana gudanarwa. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko sakamakon taron zai haifar wa kasar nan da da mai ido kuwa? Ga ra’ayoyin wasu  jama’a kamar yadda […]

Ko sakamakon Taron kasa zai haifar wa kasar nan da mai ido? 1
Ko sakamakon Taron kasa zai haifar wa kasar nan da mai ido? 1

A makon jiya ne Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya karbi gundarin shawarwarin da mahalarta Taron kasa suka cimma bayan kammala taron wanda aka kwashe kimanin wata biyar ana gudanarwa. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko sakamakon taron zai haifar wa kasar nan da da mai ido kuwa? Ga ra’ayoyin wasu  jama’a kamar yadda wakilanmu suka zanta da su:

Zai iya kawo amfani  – Alhaji danjuma Yakubu

Alhaji danjuma Yakubu: “Idan har aka yi aiki da sakamakon taron yadda ya kamata, to babu laifi. Amma, idan muka yi la’akari da irin yadda wakilan shiyyar Kudu-maso-Kudu suka rinka tayar da jijiyar wuya domin taron ya amincewa shiyyarsu samun rabon arzikin kasa mafi tsoka, sai mu ce sun yi daidai kuma suna da gaskiya ta fannin kishin kansu da talakawansu. Mu ma ‘yan Arewa mun samu irin wannan dama a baya amma muka kasa yin amfani da ita domin babu kishin Arewa a zukatan wakilanmu. Dole kuwa a rinka barinmu a baya.”