Ko sakamakon Taron kasa zai haifar wa kasar nan da mai ido? 2
A makon jiya ne Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya karbi gundarin shawarwarin da mahalarta Taron kasa suka cimma bayan kammala taron wanda aka kwashe kimanin wata biyar ana gudanarwa. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko sakamakon taron zai haifar wa kasar nan da da mai ido kuwa? Ga ra’ayoyin wasu jama’a kamar yadda […]
A makon jiya ne Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya karbi gundarin shawarwarin da mahalarta Taron kasa suka cimma bayan kammala taron wanda aka kwashe kimanin wata biyar ana gudanarwa. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko sakamakon taron zai haifar wa kasar nan da da mai ido kuwa? Ga ra’ayoyin wasu jama’a kamar yadda wakilanmu suka zanta da su:
Ba zai haifar da da mai ido ba – Umar Usman
Umar Usman: “Ni a ra’ayina Taron kasa ba zai haifarwa kasan nan da mai ido ba, dalilina kuwa shi ne tun asali ba a dora taron kan tsarin adalci ba, idan ka dubi ko wurin nada wakilai abin babu ka’ida a ciki, kuma abin ya fito da maitar jama’ar Kudu a fili, kamar kan karin wa’adin shugaban kasa, da fifita arzikin kasa da kuma lalata ko nakasa duk wani kokari da shugabannin Arewa suka yi a baya, kamar rushe tsarin kananan hukumomi.