Ko sakamakon Taron kasa zai haifar wa kasar nan da mai ido? 3
A makon jiya ne Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya karbi gundarin shawarwarin da mahalarta Taron kasa suka cimma bayan kammala taron wanda aka kwashe kimanin wata biyar ana gudanarwa. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko sakamakon taron zai haifar wa kasar nan da da mai ido kuwa? Ga ra’ayoyin wasu jama’a kamar yadda […]
A makon jiya ne Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya karbi gundarin shawarwarin da mahalarta Taron kasa suka cimma bayan kammala taron wanda aka kwashe kimanin wata biyar ana gudanarwa. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko sakamakon taron zai haifar wa kasar nan da da mai ido kuwa? Ga ra’ayoyin wasu jama’a kamar yadda wakilanmu suka zanta da su:
Babu wata fa’ida da zai kawo wa kasar nan – Ishak Tambuwal Gusau
Ishak Tambuwal Gusau: “Duk mai hankali ya san babu abin da Taron kasa zai haifar sai matsala saboda an gudanar da shi ne bisa wata manufa ta siyasa, babu matsalar da aka tattauna don talaka ko domin amfanin talaka, abin da aka tattauna bai wuce batun yadda za’ayi da arzikin kasa ba, nasu wane zai fi yawa. Amma
ba matsalar wutar lantarki ba, ko matsalar makarantu ko rashin kayan. Sai batun yaya shugaban kasa zai ci gaba da mulki.”