Ko sakamakon Taron kasa zai haifar wa kasar nan da mai ido? 4
A makon jiya ne Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya karbi gundarin shawarwarin da mahalarta Taron kasa suka cimma bayan kammala taron wanda aka kwashe kimanin wata biyar ana gudanarwa. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko sakamakon taron zai haifar wa kasar nan da da mai ido kuwa? Ga ra’ayoyin wasu jama’a kamar yadda […]
A makon jiya ne Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya karbi gundarin shawarwarin da mahalarta Taron kasa suka cimma bayan kammala taron wanda aka kwashe kimanin wata biyar ana gudanarwa. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko sakamakon taron zai haifar wa kasar nan da da mai ido kuwa? Ga ra’ayoyin wasu jama’a kamar yadda wakilanmu suka zanta da su:
Ba zai haifar da da mai ido ba – Shafi’u Gaya
Shafi’u Gaya: “A gaskiya ba na tunanin cewa wannan taron zai kawo wani ci gaba ga kasar nan saboda ba kansa farau ba. An sha gudanar da irinsa a baya amma har yau ba ta sauya zani ba. Kuma da a ce ana samun nasara da tun farko ba a kira wannan taron ba saboda da nabaya sun warware mana matsalolin tuntuni. Dalili da wannan nake ganin ba bu wani tasiri da za a samu daga wannan taron da aka kammala kwnakin baya.”