Ko samar da kudin bai daya ga kasashen Afrika Ta Yamma zai iya bunkasa tattalin arzikin kasashen?

Gamayyar kasashen Afrika Ta Yamma da suke cikin kungiyar ECOWAS na kokarin ganin yiwuwar samar da kudi na bai daya da za a rika amfani da su a kasashen. Abin tambaya a nan shi ne, shin idan an samar da wannan kudi, ko hakan zai yi tasiri wajen bunkasa tattalin arzikin kasashen? Wakilanmu sun tuntubi […]

Ko samar da kudin bai daya ga kasashen Afrika Ta Yamma zai iya bunkasa tattalin arzikin kasashen?
Ko samar da kudin bai daya ga kasashen Afrika Ta Yamma zai iya bunkasa tattalin arzikin kasashen?

Gamayyar kasashen Afrika Ta Yamma da suke cikin kungiyar ECOWAS na kokarin ganin yiwuwar samar da kudi na bai daya da za a rika amfani da su a kasashen. Abin tambaya a nan shi ne, shin idan an samar da wannan kudi, ko hakan zai yi tasiri wajen bunkasa tattalin arzikin kasashen? Wakilanmu sun tuntubi mutane daban-daban kuma ga ra’ayoyinsu:

Kudin za su yi tasiri – Abubakar Lawal

Abubakar Lawal Suleiman: “A gaskiya idan za a yi da gaskiya ne, ba shakka zai taimaka wa kasashen ECOWAS, musamman wajen bunkasa tattalin arzikinsu amma ba inda gizo ke saka ba ke nan. Don fito da wannan takardar kudi guda daya zai iya kawo cin hanci da rashawa a wadannan kasashe, musamman a nan Najeriya. Su dai Turawa hakan zai iya musu tasiri don tun farko ba su tashi da cin hanci da rashawa ba amma duk kasashe da ke wannan kungiyar ECOWAS fa sai a hankali, don ba mamaki ma kafin a gama buga kudin za su buga nasu na bogi. Saboda haka a wani gefe zai amfani kasashen, a wani gefen kuma zai haifar da cin hanci da rashawa ne kawai.”