Ko samar da kudin bai daya ga kasashen Afrika Ta Yamma zai iya bunkasa tattalin arzikin kasashen? 1

Gamayyar kasashen Afrika Ta Yamma da suke cikin kungiyar ECOWAS na kokarin ganin yiwuwar samar da kudi na bai daya da za a rika amfani da su a kasashen. Abin tambaya a nan shi ne, shin idan an samar da wannan kudi, ko hakan zai yi tasiri wajen bunkasa tattalin arzikin kasashen? Wakilanmu sun tuntubi […]

Ko samar da kudin bai daya ga kasashen Afrika Ta Yamma zai iya bunkasa tattalin arzikin kasashen? 1
Ko samar da kudin bai daya ga kasashen Afrika Ta Yamma zai iya bunkasa tattalin arzikin kasashen? 1

Gamayyar kasashen Afrika Ta Yamma da suke cikin kungiyar ECOWAS na kokarin ganin yiwuwar samar da kudi na bai daya da za a rika amfani da su a kasashen. Abin tambaya a nan shi ne, shin idan an samar da wannan kudi, ko hakan zai yi tasiri wajen bunkasa tattalin arzikin kasashen? Wakilanmu sun tuntubi mutane daban-daban kuma ga ra’ayoyinsu:

Akwai alheri a kudin bai daya – Rahina Adamu

Rahina Adamu: “Ra’ayina game da kudin bai daya da kasashen Afrika Ta Yamma ke kokarin bullo da su don harkokinsu na yau da kullum a tsakaninsu, abu ne mai kyau da kuma tattare da alherai masu yawa. daya daga cikinsu shi ne, zai ba jama’ar yankin saukin gudanar da al’amuransu, sannan kuma kalubalen da za su fuskanta musamman wurin musayar kudaden kasashen yankin zai kau. Yadda kasashen Turai suka dade suna cikin moriyar wannan lamarin daga lokacin da suka bullo da irin wannan salon, shi ma abin misali ne.”