Ko samar da kudin bai daya ga kasashen Afrika Ta Yamma zai iya bunkasa tattalin arzikin kasashen? 2
Gamayyar kasashen Afrika Ta Yamma da suke cikin kungiyar ECOWAS na kokarin ganin yiwuwar samar da kudi na bai daya da za a rika amfani da su a kasashen. Abin tambaya a nan shi ne, shin idan an samar da wannan kudi, ko hakan zai yi tasiri wajen bunkasa tattalin arzikin kasashen? Wakilanmu sun tuntubi […]
Gamayyar kasashen Afrika Ta Yamma da suke cikin kungiyar ECOWAS na kokarin ganin yiwuwar samar da kudi na bai daya da za a rika amfani da su a kasashen. Abin tambaya a nan shi ne, shin idan an samar da wannan kudi, ko hakan zai yi tasiri wajen bunkasa tattalin arzikin kasashen? Wakilanmu sun tuntubi mutane daban-daban kuma ga ra’ayoyinsu:
Tattalin arzikin zai bunkasa – Babangida Usman
Hon. Babangida Usman: “Ni a tawa fahimtar, ina ganin bullo da kudi na bai daya da kasashen ECOWAS suke son yi zai bunkasa tattalin arzikin wadannan kasashe, domin kuwa ko fasfo da wadannan kasashe suka yi na bai daya ya yi tasiri. Idan aka lura da irin kasashen Turai wadanda tattalin arzikinsu ya karye, da suka yi irin wannan tsari yanzu duk sun ci gaba a duniya wajen karfin tattalin arzikin kasa. Ina da yakinin cewa muddin kasashen suka bullo da wannan tsari, za su ci gaba wajen hadin kai da kuma bunkasar tattalin arzikin kasa. Don haka ni ina ganin ba sai ma an tsaya neman wata shawara ba saboda wannan tsari, tsari ne mai kyau.”