Ko samar da kudin bai daya ga kasashen Afrika Ta Yamma zai iya bunkasa tattalin arzikin kasashen? 3
Gamayyar kasashen Afrika Ta Yamma da suke cikin kungiyar ECOWAS na kokarin ganin yiwuwar samar da kudi na bai daya da za a rika amfani da su a kasashen. Abin tambaya a nan shi ne, shin idan an samar da wannan kudi, ko hakan zai yi tasiri wajen bunkasa tattalin arzikin kasashen? Wakilanmu sun tuntubi […]
Gamayyar kasashen Afrika Ta Yamma da suke cikin kungiyar ECOWAS na kokarin ganin yiwuwar samar da kudi na bai daya da za a rika amfani da su a kasashen. Abin tambaya a nan shi ne, shin idan an samar da wannan kudi, ko hakan zai yi tasiri wajen bunkasa tattalin arzikin kasashen? Wakilanmu sun tuntubi mutane daban-daban kuma ga ra’ayoyinsu:
Tasirin kudin ya danganta da darajarsu – Musa Hantsu
Musa M. Hantsu Agyaragu: “Ni dai a fahimta ta da kuma ra’ayina shi ne, a gaskiya idan har kudin zai yi daraja kamar yadda wasu gamayyar kasashen Turai suka hada kudinsu suka daukaka suka yi daraja a duniya baki daya. Idan kudin kasashen Afrika Ta Yamma ma za a hada su su yi daraja, yadda duk inda ka shiga a duniya za ka samu su da darajarua da komai to, hakan ya yi kyau, zai amfane mu ya kuma bunkasa tattalin arzikinmu, babu shakka. Amma idan ba zai yi daraja ba, to a bar mu yadda muke kawai.”