Ko samar da kudin bai daya ga kasashen Afrika Ta Yamma zai iya bunkasa tattalin arzikin kasashen? 4

Gamayyar kasashen Afrika Ta Yamma da suke cikin kungiyar ECOWAS na kokarin ganin yiwuwar samar da kudi na bai daya da za a rika amfani da su a kasashen. Abin tambaya a nan shi ne, shin idan an samar da wannan kudi, ko hakan zai yi tasiri wajen bunkasa tattalin arzikin kasashen? Wakilanmu sun tuntubi […]

Ko samar da kudin bai daya ga kasashen Afrika Ta Yamma zai iya bunkasa tattalin arzikin kasashen? 4
Ko samar da kudin bai daya ga kasashen Afrika Ta Yamma zai iya bunkasa tattalin arzikin kasashen? 4

Gamayyar kasashen Afrika Ta Yamma da suke cikin kungiyar ECOWAS na kokarin ganin yiwuwar samar da kudi na bai daya da za a rika amfani da su a kasashen. Abin tambaya a nan shi ne, shin idan an samar da wannan kudi, ko hakan zai yi tasiri wajen bunkasa tattalin arzikin kasashen? Wakilanmu sun tuntubi mutane daban-daban kuma ga ra’ayoyinsu:

Kudin za su yi tasiri – Isma’ila Hussaini

Isma’ila Hussaini: “Wannan babban alheri ne a tsakanin kasashen Afrika Ta Yamma, wanda ba zai tsaya a kan bunkasa fannin tattalin arzikin yankin kadai ba, wata dama ce wadda za su yi amfani da ita domin kara dankon zumuncin da ke tsakaninsu. Babban abin da za ka lura da shi shi ne, da dadewa wadannan kasashen sun dade suna mu’amala da juna ba tare da la’akari da bambance-bambancen harsunan da ke tsakanin kasashen da suke renon kasar Faransa da na Birtaniya ba.”