Ko samar da kudin bai daya ga kasashen Afrika Ta Yamma zai iya bunkasa tattalin arzikin kasashen? 5
Gamayyar kasashen Afrika Ta Yamma da suke cikin kungiyar ECOWAS na kokarin ganin yiwuwar samar da kudi na bai daya da za a rika amfani da su a kasashen. Abin tambaya a nan shi ne, shin idan an samar da wannan kudi, ko hakan zai yi tasiri wajen bunkasa tattalin arzikin kasashen? Wakilanmu sun tuntubi […]
Gamayyar kasashen Afrika Ta Yamma da suke cikin kungiyar ECOWAS na kokarin ganin yiwuwar samar da kudi na bai daya da za a rika amfani da su a kasashen. Abin tambaya a nan shi ne, shin idan an samar da wannan kudi, ko hakan zai yi tasiri wajen bunkasa tattalin arzikin kasashen? Wakilanmu sun tuntubi mutane daban-daban kuma ga ra’ayoyinsu:
Tsarin kudin ba zai yi tasiri ba – Malam Haruna
Malam Haruna Adaji: “A gani na wannan tsari na neman yin amfani da kudi bai daya a kasashen ECOWAS ba zai yi tasiri ba, domin kuwa idan ba a yi da gaske ba ma sai duk kasashen sun ci baya. Misali, kudin Euro, inda aka samu masu karfin tattalin arzikin kasa irin Faransa; tattalin arzikinsu ya habaka wasu kuma irin su Portugal da Greece, nasu ya durkushe. Wannan tsari na samar da kudin bai daya ba zai haifar wa wadannan kasashe da mai ido ba.”