Ko samun kujerar kwamitin tsaro ta Majalisar dinkin Duniya da Najeriya ta yi zai amfani kasar da al’ummarta?
A makon da ya wuce ne Najeriya ta samu zama daya daga cikin membobin kwamitin tsaro na Majalisar dinkin Duniya, a yayin da kasar Saudiyya ta ce ba ta bukatar wannan kujera da aka ba ta. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko wannan kujera za ta zama mai amfani ga Najeriya da al’umarta? […]
A makon da ya wuce ne Najeriya ta samu zama daya daga cikin membobin kwamitin tsaro na Majalisar dinkin Duniya, a yayin da kasar Saudiyya ta ce ba ta bukatar wannan kujera da aka ba ta. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko wannan kujera za ta zama mai amfani ga Najeriya da al’umarta? Ga abin da mutane suka bayyana ta hannun wakilanmu na sassan kasar nan:
Al’amarin yana da kyau ga Najeriya
– Abdulwasi Salawuddin
Abdulwasi Salawuddin: “Samun Najeriya ta shiga cikin wannan kwamitin yana da kyau kwarai da gaske, domin da sako take bayarwa amma yanzu tana ciki ne tsumbul, ba wata kumbiya-kumbiya da za a yi ba da saninta ba, kuma daga yanzu batun wani ya yi magana a madadinta ya kau, sai dai ta tsaya wa kanta kuma har ta tsaya wa wata kasar; sabanin abin da ke faruwa a da. Ka ga da sako take bayarwa amma yanzu sai dai wata kasa ko kasashe su raba da ita kuma da ma ita ce babbar kasa mai tasiri a nahiyar Afrika. Ni dai a nawa ra’ayin yana da amfani kwarai da gaske.”