Ko samun kujerar kwamitin tsaro ta Majalisar dinkin Duniya da Najeriya ta yi zai amfani kasar da al’ummarta?1

A makon da ya wuce ne Najeriya ta samu zama daya daga cikin membobin kwamitin tsaro na Majalisar dinkin Duniya, a yayin da kasar Saudiyya ta ce ba ta bukatar wannan kujera da aka ba ta. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko wannan kujera za ta zama mai amfani ga Najeriya da al’umarta? […]

Ko samun kujerar kwamitin tsaro ta Majalisar dinkin Duniya da Najeriya ta yi zai amfani kasar da al’ummarta?1
Ko samun kujerar kwamitin tsaro ta Majalisar dinkin Duniya da Najeriya ta yi zai amfani kasar da al’ummarta?1

A makon da ya wuce ne Najeriya ta samu zama daya daga cikin membobin kwamitin tsaro na Majalisar dinkin Duniya, a yayin da kasar Saudiyya ta ce ba ta bukatar wannan kujera da aka ba ta. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko wannan kujera za ta zama mai amfani ga Najeriya da al’umarta? Ga abin da mutane suka bayyana ta hannun wakilanmu na sassan kasar nan:

Babu wani alfanu da Nijeriya za ta samu – Iliyasu Muhammad
Alhaji Iliyasu Muhammad: “Maganar wakilcin da Najeriya ta samu a kwamitin tsaro na Majalisar dinkin Duniya, ba wani bakon abu ne a siyasar duniya ba. Kuma a kullum manyan kasashen yamma ba su yarda su fadi su kadai, don haka duk lokacin da ka ga manyan kasashen yamma sun gayyaci wasu kasashen Afrika zuwa irin wannan waje, to akwai dalili. Don haka ni a ganina babu wani alfanu da Najeriya za ta samu don ta zama wakiliya a kwamitin tsaro na Majalisar dinkin Duniya, sai dai ci baya. Kasancewar Najeriya a kungiyar kasashen Afrika ya fi ta zama wakiliya a kwamitin tsaro na Majalisar dinkin Duniya mahimmanci.”

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya