Ko samun kujerar kwamitin tsaro ta Majalisar dinkin Duniya da Najeriya ta yi zai amfani kasar da al’ummarta?2

A makon da ya wuce ne Najeriya ta samu zama daya daga cikin membobin kwamitin tsaro na Majalisar dinkin Duniya, a yayin da kasar Saudiyya ta ce ba ta bukatar wannan kujera da aka ba ta. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko wannan kujera za ta zama mai amfani ga Najeriya da al’umarta? […]

Ko samun kujerar kwamitin tsaro ta Majalisar dinkin Duniya da Najeriya ta yi zai amfani kasar da al’ummarta?2
Ko samun kujerar kwamitin tsaro ta Majalisar dinkin Duniya da Najeriya ta yi zai amfani kasar da al’ummarta?2

A makon da ya wuce ne Najeriya ta samu zama daya daga cikin membobin kwamitin tsaro na Majalisar dinkin Duniya, a yayin da kasar Saudiyya ta ce ba ta bukatar wannan kujera da aka ba ta. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko wannan kujera za ta zama mai amfani ga Najeriya da al’umarta? Ga abin da mutane suka bayyana ta hannun wakilanmu na sassan kasar nan:

Akwai alfanu ga Najeriya – Kabir danbauchi
Kabir danbauchi: “Ba shakka zabar Najeriya da aka yi cikin wannan kwamitin tsaro na Majilisar dinkin Duniya yana da kyau kwarai da gaske. Abu ne da ya kamata a ce an yi tun da dadewa, domin duk abin da ake son kasa ta mallaka domin ta samu shiga cikin wannan kwamitin Najeriya tana da shi, domin saka ta cikin wannan kwamitin tamkar an saka nahiyar Afrika ne. Batun ganin amfaninta a cikin wanna kwamitin ba abu ne da za a ce za a gani yanzu-yanzu ba, domin samun kanta cikin wannan wuri wata babbar martaba ce ba ga idanun Afrika kawai ba, a idanun duniya gaba daya. Daga yanzu ba wata munakisa da za a yi wa wata kasar Afrika ba tare da sanin Najeriya ba kuma ba za ta kyale ba, domin ko kafin ta shiga cikin wannan wuri ita ce kamar uwargijiyar duk wata kasa ta Afrika.”

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya