Ko samun kujerar kwamitin tsaro ta Majalisar dinkin Duniya da Najeriya ta yi zai amfani kasar da al’ummarta?3
A makon da ya wuce ne Najeriya ta samu zama daya daga cikin membobin kwamitin tsaro na Majalisar dinkin Duniya, a yayin da kasar Saudiyya ta ce ba ta bukatar wannan kujera da aka ba ta. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko wannan kujera za ta zama mai amfani ga Najeriya da al’umarta? […]
A makon da ya wuce ne Najeriya ta samu zama daya daga cikin membobin kwamitin tsaro na Majalisar dinkin Duniya, a yayin da kasar Saudiyya ta ce ba ta bukatar wannan kujera da aka ba ta. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko wannan kujera za ta zama mai amfani ga Najeriya da al’umarta? Ga abin da mutane suka bayyana ta hannun wakilanmu na sassan kasar nan:
Akwai amfani a kujerar
– Musa danbirni
Alhaji Musa danbirni: “Ni a ganina, ya dangana da yadda Najeriya ko in ce gwamnatin Najeriya ta dauki wannan matsayi da aka ba ta da muhimmanci. Ina nufin ta wajen tsayawarta ta ga ta yi abin da ya dace wajen kare hakkin raunanan kasashe da bayyana ra’ayinta a gaban majalisar, wanda zai yi amfani da ciyar da Najeriya da sauran kasashen Afirka ba tare da tsoro ko shayi ba. Idan aka samu haka, tabbas matsayin alheri ne ga kasar nan.”