Ko samun kujerar kwamitin tsaro ta Majalisar dinkin Duniya da Najeriya ta yi zai amfani kasar da al’ummarta?4
A makon da ya wuce ne Najeriya ta samu zama daya daga cikin membobin kwamitin tsaro na Majalisar dinkin Duniya, a yayin da kasar Saudiyya ta ce ba ta bukatar wannan kujera da aka ba ta. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko wannan kujera za ta zama mai amfani ga Najeriya da al’umarta? […]
A makon da ya wuce ne Najeriya ta samu zama daya daga cikin membobin kwamitin tsaro na Majalisar dinkin Duniya, a yayin da kasar Saudiyya ta ce ba ta bukatar wannan kujera da aka ba ta. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko wannan kujera za ta zama mai amfani ga Najeriya da al’umarta? Ga abin da mutane suka bayyana ta hannun wakilanmu na sassan kasar nan:
A wajen talakan Najeriya babu wani amfani – Habibu Abubakar
Alhaji Habibu Abubakar: “Babu wani alfanu da Najeriya za ta samu don ta zama wakiliya a kwamitin tsaro na Majalisar dinkin Duniya. Idan ma za a sami wani alfanu to zai tsaya ne a kan matakin Shugaban kasa da ministocinsa da jakadunsa, ta yadda za su kara samun suna a duniya, su sami damar ci gaba da kwashe dukiyar Najeriya. Amma a wajen talakan Najeriya babu wani alfanu da zai samu don Najeriya ta zama wakiliya a kwamitin tsaro na majalisar dinkin Duniya. Domin ba wannan ne damuwar talakan Najeriya ba. Halin da talakan
Najeriya yake ciki a yanzu, sai dai a ci gaba da addu’a kawai.”