Ko samun kujerar kwamitin tsaro ta Majalisar dinkin Duniya da Najeriya ta yi zai amfani kasar da al’ummarta?5
A makon da ya wuce ne Najeriya ta samu zama daya daga cikin membobin kwamitin tsaro na Majalisar dinkin Duniya, a yayin da kasar Saudiyya ta ce ba ta bukatar wannan kujera da aka ba ta. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko wannan kujera za ta zama mai amfani ga Najeriya da al’umarta? […]
A makon da ya wuce ne Najeriya ta samu zama daya daga cikin membobin kwamitin tsaro na Majalisar dinkin Duniya, a yayin da kasar Saudiyya ta ce ba ta bukatar wannan kujera da aka ba ta. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko wannan kujera za ta zama mai amfani ga Najeriya da al’umarta? Ga abin da mutane suka bayyana ta hannun wakilanmu na sassan kasar nan:
Kujerar za ta zama alheri ga Najeriya – Hafizu Alkasim
Alhaji Hafizu Alkasim: “Ina da ra’ayin cewa shigarta wannan kwamiti zai haifar da alheri ga Najeriya. Dalilina a nan kuwa shi ne duk da cewa sauran kasashen da ke wannan kwamitin na majalisar manyan kasashe ne, to ai mu ma idan an duba Najeriya babbar kasa ce a wajenmu nan Afirka. Kuma ko babu komai ma ai su ma sauran kasashen da haka suka fara daga matsayi na kasa, har suka kai wannan matsayinsu na yanzu.”