Ko sau dari za a dage zabe ’yan Najeriya ba za su zabi PDP ba – Salisu Ibrahim
dan Majalisar Dokoki ta Jihar Kano mai wakiltar karamar Hukumar Doguwa Alhaji Salisu Ibrahim Muhammad ya ce ko sau dari za a dage zabe ’yan Najeriya ba za su zabi Jam’iyyar PDP ba. Alhaji Salisu Ibrahim ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu kan dage lokacin zabe da Hukumar Zabe ta […]
dan Majalisar Dokoki ta Jihar Kano mai wakiltar karamar Hukumar Doguwa Alhaji Salisu Ibrahim Muhammad ya ce ko sau dari za a dage zabe ’yan Najeriya ba za su zabi Jam’iyyar PDP ba.
Alhaji Salisu Ibrahim ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu kan dage lokacin zabe da Hukumar Zabe ta kasa (INEC) ta yi a ranar Asabar da ta gabata. Ya ce “dage zaben ya zo mana da mamaki kwarai da gaske saboda a makon jiya ne Majalisar kasa ta yi taro kan lamarin kuma ta ba ’yan Najeriya tabbacin cewa ba za a dage zaben ba, za a gudanar da shi a lokacin da aka tsara. Amma abin mamaki sai ga shi anzo an dage zaben.”
Alhaji Salisu Ibrahim ya ce irin abubuwan da suke tafiya a Najeriya na nuna cewa a shirye ’yan Najeriya suke su samu canjin gwamnati. Saboda haka ko sau nawa za a dage zabe ’yan Najeriya ba za su zabi Jam’iyyar PDP ba a kowane mataki domin sun gaji da halin da suke ciki na matsi da talauci da rashin tsaro a karkashin wannan gwamnati.
Ya ce, jam’iyya mai mulki ta hango faduwa ne a zaben shi ya sanya suka dage zaben. Ya yi kira ga al’ummar Najeriya da kada su yi fushi saboda dage zaben, domin mai nasara ba ya fushi, “Ko sau dari za a dage wannan zabe, mu bi su har Allah Ya kawo ranar da za a yi zaben mu samu a canja wannan gwamnati,” inji shi