Ko sayar da matatun fetur alfanu ne ga Najeriya?
A kwanakin baya ne Gwamnatin Tarayya ta ce za ta sayar da matatun fetur din Najeriya nan da watanni hudu masu zuwa. Abin tambayar a nan shi ne, shin ko hakan zai zama mai alfanu ga al’ummar Najeriya? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kamar haka: Babu fa’ida ga sayar da su – Hussaina AbdullahiBashir […]
A kwanakin baya ne Gwamnatin Tarayya ta ce za ta sayar da matatun fetur din Najeriya nan da watanni hudu masu zuwa. Abin tambayar a nan shi ne, shin ko hakan zai zama mai alfanu ga al’ummar Najeriya? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kamar haka:
Babu fa’ida ga sayar da su – Hussaina Abdullahi
Bashir Yahuza Malumfashi, a Gusau
Hussaina Abdullahi: “Ni dai a ganina, bai kamata a sayar da matatun mai na Najeriya ba, domin kuwa yin haka babu wani alfanu da zai kawo wa al’umma. Wani abu da nake ganin zai faru shi ne, idan ma an tashi sayar da su, ba za a sayar da su da kudi masu kima ba, za a cefanar da su ne kamar kyauta. Maimakon haka, ya kamata a gyara su, a inganta su, sannan a ci gaba da aiki da su, wanda haka zai sanya a daina shigo da tataccen mai daga kasashen waje. Yin haka zai zama mai amfani ga kasa da kuma al’umma gaba daya.”