Ko sayar da matatun fetur alfanu ne ga Najeriya? 1
A kwanakin baya ne Gwamnatin Tarayya ta ce za ta sayar da matatun fetur din Najeriya nan da watanni hudu masu zuwa. Abin tambayar a nan shi ne, shin ko hakan zai zama mai alfanu ga al’ummar Najeriya? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kamar haka: A gyara su ba sayarwa ba – Jamila AbubakarBashir […]
A kwanakin baya ne Gwamnatin Tarayya ta ce za ta sayar da matatun fetur din Najeriya nan da watanni hudu masu zuwa. Abin tambayar a nan shi ne, shin ko hakan zai zama mai alfanu ga al’ummar Najeriya? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kamar haka:
A gyara su ba sayarwa ba – Jamila Abubakar
Bashir Yahuza Malumfashi, a Gusau
Jamila Abubakar: “Ni a ra’ayina game da batun sayar da matatun man fetur na kasa, bai kamata a sayar da su ba, domin kuwa ba hakan ne ya fi muhimmanci ba. Kamata ya yi a fidda kudi, a kira kwararru daga waje su gyara su. Haka kuma, bayan an gyara sai a samu amintattun mutane, a ba su amanar kula da su. A sanya doka mai tsauri ga duk wanda ya yi almundahana wajen gudanar da su. Haka zai sanya su zama masu aiki, masu amfani ga ’yan kasa, domin kuwa za su wadata kasa da tataccen mai, ba sai an fita waje an sawo ba. Ta haka za a samu ci gaba sosai kuma a samu rahusar albarkatun man fetur a kasa.