Ko sayar da matatun fetur alfanu ne ga Najeriya? 2
A kwanakin baya ne Gwamnatin Tarayya ta ce za ta sayar da matatun fetur din Najeriya nan da watanni hudu masu zuwa. Abin tambayar a nan shi ne, shin ko hakan zai zama mai alfanu ga al’ummar Najeriya? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kamar haka: Sayar su ba alheri ba ne – Muhammad dahiruRabilu […]
A kwanakin baya ne Gwamnatin Tarayya ta ce za ta sayar da matatun fetur din Najeriya nan da watanni hudu masu zuwa. Abin tambayar a nan shi ne, shin ko hakan zai zama mai alfanu ga al’ummar Najeriya? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kamar haka:
Sayar su ba alheri ba ne – Muhammad dahiru
Rabilu Abubakar, a Gombe
Muhammad dahiru: “Ni a nawa ra’ayin, sayar da matatun man fetur din kasar nan ba alheri ba ne, domin kayan al’umma ne ba na gwamnati ba. Don haka kafin a sayar, ya dace sai an nemi ra’ayoyin al’umma tukun. Idan jama’a ba su gamsu ba, bai kamata a sayar ba saboda suna da hakki a kai kuma ita gwamnatin a lokacin da take neman sake zarcewa a kujera ai yawo suke yi suna neman goyon bayan jama’a. Me zai hana yanzu ma su nemi ra’ayin jama’a tukunna?”