Ko sayar da matatun fetur alfanu ne ga Najeriya? 3

A kwanakin baya ne Gwamnatin Tarayya ta ce za ta sayar da matatun fetur din Najeriya nan da watanni hudu masu zuwa. Abin tambayar a nan shi ne, shin ko hakan zai zama mai alfanu ga al’ummar Najeriya? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kamar haka: Sayar da su alheri ne – Ibrahim dalhaRabilu Abubakar, […]

Ko sayar da matatun fetur alfanu ne ga Najeriya? 3
Ko sayar da matatun fetur alfanu ne ga Najeriya? 3

A kwanakin baya ne Gwamnatin Tarayya ta ce za ta sayar da matatun fetur din Najeriya nan da watanni hudu masu zuwa. Abin tambayar a nan shi ne, shin ko hakan zai zama mai alfanu ga al’ummar Najeriya? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kamar haka:

Sayar da su alheri ne – Ibrahim dalha
Rabilu Abubakar, a Gombe

Ibrahim Dalha (Anko): “Sayar da matatun man fetur din kasar nan alheri ne ga talakawa, domin zai kawo wa talakawan mafita ta hanyoyi da yawa. Dalilina shi ne, idan gwamnati ta sayar da su, duk ’ya’yan talakwan da suka rasa aiki dole za su samu aiki tun da za su koma hannun ’yan kasuwa ko kamfanoni. Don haka idan za a ji shawarata, ina mai kira ga Gwamnatin Tarayyar da ta gaggauta sayarwa don kar daga baya ita gwamnatin ta yi tunanin cewa ’ya’yan talakawa za su iya amfana, ta canja ra’ayi.”