Ko sayar da matatun fetur alfanu ne ga Najeriya? 4
A kwanakin baya ne Gwamnatin Tarayya ta ce za ta sayar da matatun fetur din Najeriya nan da watanni hudu masu zuwa. Abin tambayar a nan shi ne, shin ko hakan zai zama mai alfanu ga al’ummar Najeriya? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kamar haka: Ya dace a sayar da su – Tijjani TankoMuhammad […]
A kwanakin baya ne Gwamnatin Tarayya ta ce za ta sayar da matatun fetur din Najeriya nan da watanni hudu masu zuwa. Abin tambayar a nan shi ne, shin ko hakan zai zama mai alfanu ga al’ummar Najeriya? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kamar haka:
Ya dace a sayar da su
– Tijjani Tanko
Muhammad danladi Ibrahim, a Minna
Alhaji Tijjani Tanko Fari: “Sayar da matatun man fetur ga ’yan kasuwa abu ne da ya dace a yi da dadewa. Rashin daukar wannan matakin tun tuni ne ya yi sanadiyyar jefa wannan kasar cikin halin da ta samu kanta. Idan ka yi nazari a hankali, za ka ga cewar ’yan kasuwa ne ke gudanar da irin wadannan al’amuran. Rawar da gwamnati ta kamata ta taka, shi ne ta sa ido yadda ya kamata, domin ganin komai yana tafiya don kar a cuci mutane; wato ’yan kasuwan su ci karensu babu babbaka.”