Ko sayar da matatun fetur alfanu ne ga Najeriya? 5

A kwanakin baya ne Gwamnatin Tarayya ta ce za ta sayar da matatun fetur din Najeriya nan da watanni hudu masu zuwa. Abin tambayar a nan shi ne, shin ko hakan zai zama mai alfanu ga al’ummar Najeriya? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kamar haka: Bai dace a sayar da matatun ba – Malam […]

Ko sayar da matatun fetur alfanu ne ga Najeriya? 5
Ko sayar da matatun fetur alfanu ne ga Najeriya? 5

A kwanakin baya ne Gwamnatin Tarayya ta ce za ta sayar da matatun fetur din Najeriya nan da watanni hudu masu zuwa. Abin tambayar a nan shi ne, shin ko hakan zai zama mai alfanu ga al’ummar Najeriya? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kamar haka:

Bai dace a sayar da matatun ba – Malam Auwal
Muhammad danladi Ibrahim, a Minna

Malam Auwal Ahmad: “Sam bai dace gwamnati ta sayar wa ’yan kasuwa wadannan matatun ba. Dalili kuwa shi ne, ba za a sayar wa wadanda suka cancanta ba, karnukan farautar su ne za su mika wa matatun bayan sun karya kudinsu. Bari in ba ka misali da Hukumar Samar Da Lantarki Ta kasa, an dade ana kashe wa kamfanin kudi, da aka tashi sayar da kamfanin sai aka sayar a kudin da ba su taka kara suka karya ba. Abin takaiciku ma shi ne, ba su biya kudin gaba daya ba, aka ba su kamfanin.”