Ko sayar da matatun fetur alfanu ne ga Najeriya? 6
A kwanakin baya ne Gwamnatin Tarayya ta ce za ta sayar da matatun fetur din Najeriya nan da watanni hudu masu zuwa. Abin tambayar a nan shi ne, shin ko hakan zai zama mai alfanu ga al’ummar Najeriya? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kamar haka: Sayar da su na da alfanu – Tasi’u dangataNasiru […]
A kwanakin baya ne Gwamnatin Tarayya ta ce za ta sayar da matatun fetur din Najeriya nan da watanni hudu masu zuwa. Abin tambayar a nan shi ne, shin ko hakan zai zama mai alfanu ga al’ummar Najeriya? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kamar haka:
Sayar da su na da alfanu – Tasi’u dangata
Nasiru Bello, a Sakkwato
Tasi’u dangata Gusau: “Sayar da matatun mai na kasar nan yana da alfanu, don shi talakan Najeriya ya dade da sanin an sayar da su, kudinsu ne kawai ba a karba ba, tun da yanzu ana bukatar karbar kudin, to gara a karba din ko kila zai samu sauki daga wadanda suka mallake su a yanzu. Ai talakkan kasar nan dole ne ya so a sayar da su, don shi bai san amfaninsu ba. Na daya dai sun lalace da dadewa kuma ba a iya gyara su kuma ba a iya canja su don kada sata ta yi sauki. To ka ga ai tunda Allah Ya kawo masu dubarar saidawa, gara su yi kila sauki ne zai zo tun da kasuwanci ne za a fara da su.”