Ko sayar da matatun fetur alfanu ne ga Najeriya? 7

A kwanakin baya ne Gwamnatin Tarayya ta ce za ta sayar da matatun fetur din Najeriya nan da watanni hudu masu zuwa. Abin tambayar a nan shi ne, shin ko hakan zai zama mai alfanu ga al’ummar Najeriya? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kamar haka: Babu alfanu ga sayar da su – Sharif UsmanNasiru […]

Ko sayar da matatun fetur alfanu ne ga Najeriya? 7
Ko sayar da matatun fetur alfanu ne ga Najeriya? 7

A kwanakin baya ne Gwamnatin Tarayya ta ce za ta sayar da matatun fetur din Najeriya nan da watanni hudu masu zuwa. Abin tambayar a nan shi ne, shin ko hakan zai zama mai alfanu ga al’ummar Najeriya? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kamar haka:

Babu alfanu ga sayar da su – Sharif Usman
Nasiru Bello, a Sakkwato

Sharif Usman Baban Umma: “Gaskiya ba wani alfanu ga sayar da matatun man kasar nan, domin wannan ci baya ne na karshe a Nijeriya. Komai a ce an sayar, wane lalaci ne wannnan! Matatun mai na kasa gaba dayansu kamata ya yi a gyara su a kuma karo wasu, ba wai a sayar ba. Ina amfanin a gina mai a kasar nan amma kuma a je wata kasa tace shi? In yanzu aka gyara su mutane za su samu aikin yi sosai amma in har aka sayar da su, mutanen da suka saya in har nan za su yi aiki da su to da mutanensu za su zo mu a nan sai dai mu zama bayi. Ka ga ai wannan bai dace ba a kawo mana wulakanci kuma wai da sunan muna da arziki.