Ko shekara 50 Ganduje ya yi ba zai iya yin ayyukan Kwankwaso ba-Nuradeen
Shugaban ayyuka na kungiyar Kwankwasiyya Ta kasa kuma Shugaban Kwankwasiyya reshen Jihar Filato Alhaji Nuradeen Muhammad Inuwa, ya bayyana cewa ko shekara 50 Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje zai yi yana Gwamna, ba zai iya yin ayyukan raya kasa da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi ba a shekara hudu da ya yi […]

Shugaban ayyuka na kungiyar Kwankwasiyya Ta kasa kuma Shugaban Kwankwasiyya reshen Jihar Filato Alhaji Nuradeen Muhammad Inuwa, ya bayyana cewa ko shekara 50 Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje zai yi yana Gwamna, ba zai iya yin ayyukan raya kasa da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi ba a shekara hudu da ya yi a matsayin Gwamnan Jihar ba. Alhaji Nuradeen Muhammad Inuwa ya bayyana haka ne, a lokacin da yake zantawa da Aminiya takaddamar da ke faruwa yanzu, a tsakanin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso a Jihar Kano.
Ya ce abubuwan da suke faruwa a yanzu, a tsakanin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da tsohon Gwamnan Jihar, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso abubuwa ne marasa dadi.
Ya kara da cewa, yanzu Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya fito karara yana yaki da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, duk da halaccin da ya nuna masa. Kuma ya zo yana kokarin soke abubuwan alherin da ya yi.
Ya ce kokarin da Gwamna Ganduje yake yi a ’yan kwanakin nan na cire sunayen Kwankwasiyya a jikin ayyukan alheri da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi a lokacin da yake Gwamna a Jihar Kano, abin takaici ne.
“Abin da Gwamna Ganduje bai gane ba shi ne zai iya canja sunayen ayyukan da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi, amma ba zai iya cewa ba shi ne ya yi wadannan ayyuka ba. Lokacin da Kwankwaso ya zo kan kujerar Gwamnan Jihar Kano, bai canja aikin wani tsohon Gwamna ba, ya yi nasa ayyuka ne inda ya mayar da birnin Kano kamar birnin Landan. Kuma duk inda mutum ya duba a Jihar Kano, zai ga ayyukan da ya yi. Don haka da Gwamna Ganduje yana kaunar mutanen Kano sai ya kawo nasa sababbin ayyukan, maimakon canja sunayen ayyukan da Kwankwaso ya yi.’’
Alhaji Nuradeen ya ce ayyukan da Sanata Kwankwaso ya yi, a lokacin da yake Gwamnan Jihar Kano su ne suka sanya al’ummar jihar da Najeriya suke nuna masa kauna.
Ya ce babu shakka wannan abu da Gwamna Ganduje yake yi, illa ce ga siyasarsa kuma babbar nasara ce ga Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.