Ko Shugaba Jonathan zai iya wadata kasar nan da lantarki a bana?
Alhaji Abdulkarim Allahnana (Oscar), dan takarar shugabancin karamar Hukumar Keana, Jihar Nasarawa: “Duk wanda ya yi maka alkawari a jiya bai iya cikawa ba, yaushe idan ya sake yi maka wani a yau za ka yi tsammanin zai iya cikawa a gobe? Wannan alkawarin da Jonathan ya yi, ba zai iya cika shi ba, domin […]
Alhaji Abdulkarim Allahnana (Oscar), dan takarar shugabancin karamar Hukumar Keana, Jihar Nasarawa: “Duk wanda ya yi maka alkawari a jiya bai iya cikawa ba, yaushe idan ya sake yi maka wani a yau za ka yi tsammanin zai iya cikawa a gobe? Wannan alkawarin da Jonathan ya yi, ba zai iya cika shi ba, domin kuwa babu inda ya taba cika wani alkawari. Kowa ya shaida, tun da ya hau mulki yake yin alkawura amma bai taba cikawa ba.
Ba zai iya wadatar da lantarki ba – Isyaka Muhammad
Isyaka Muhammad Hadeja: “Gaskiya ba zai iya wadata kasar nan da wutar lantarki cikin shekarar nan ba kamar yadda ya yi alkawari. Dalili, lokacin da aka kara kudin man fetur, sun yi mana alkawari cewa wata uku ’yan Najeriya za mu gani a kasa kuma ga shi har yanzu ba mu ga komai ba. Gaskiya Jonathan ba ya cika alkawari.”