Ko Shugaba Jonathan zai iya wadata kasar nan da lantarki a bana?7
A kasafin kudin bana ne Shugaba Goodluck Jonathan ya dauki alwashin cewa nan da zuwa watan Yuni na bana, zai wadata kasar nan da wutar lantarki. Abin tambaya a nan shi ne, idan aka yi la’akari da alkawuran da ya taba yi a baya game da lantarkin, ko a wannan karon zai iya cika alkawari? […]
A kasafin kudin bana ne Shugaba Goodluck Jonathan ya dauki alwashin cewa nan da zuwa watan Yuni na bana, zai wadata kasar nan da wutar lantarki. Abin tambaya a nan shi ne, idan aka yi la’akari da alkawuran da ya taba yi a baya game da lantarkin, ko a wannan karon zai iya cika alkawari? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban a kan batun kuma ga abin da suke cewa:
Ba zai iya samar da wutar lantarki ba – Salisu Iliya
Salisu Iliya: “Ya kamata talaka ya manta da batun samuwar wutar lantarki a kasar nan, domin wadannan shugabannin ba talaka ne a gabansu ba. Sun san idan aka
sami tsayayyar wutar lantarki abubuwan rayuwa za su yi wa talaka sauki. To su kuma hakan ne ba su son gani. Sun fi so a kullum su ga talaka cikin wahala. Mun tabbatar ba kudin da za a samar da wutar lantarkin ne babu a kasar nan ba, kasar nan tana da arziki sosai amma kasancewar manyanmu mahandama ne, da a ce sun samar da wutar sun gwammmace su wawushe kudin su ci daga su sai ’ya’yansu.”