Ko soke Post UTME (Jarabawar cancantar shiga makarantun gaba da sakandare) ya dace kuwa?
A kwanakin baya ne hukumomi suka bayyana soke Post UTME (Jarabawar cancantar shiga makarantun gaba da sakandare), inda a yanzu daliban da suka samu makin da ya dace daga jarabawar JAMB, za su cancanci shiga jami’a da sauran makarantun gaba da sakandare kai tsaye. Abin tambaya a nan shi ne, shin wannan mataki na soke […]
A kwanakin baya ne hukumomi suka bayyana soke Post UTME (Jarabawar cancantar shiga makarantun gaba da sakandare), inda a yanzu daliban da suka samu makin da ya dace daga jarabawar JAMB, za su cancanci shiga jami’a da sauran makarantun gaba da sakandare kai tsaye. Abin tambaya a nan shi ne, shin wannan mataki na soke jarabawar ko ya dace kuwa? Wakilanmu sun tattauna da mabambantan mutane, wadanda suka bayyana ra’ayoyinsu kamar haka:
Soke jarabawar ya dace – Ibrahim Zaki
Bashir Yahuza Malumfashi, a Abuja
Malam Ibrahim Zaki: “Wannan mataki na soke jarabawar Post UTME ya dace kwarai da gaske kuma na yi murna da shi. Dalilina na fadin haka shi ne, dama jarabawar ta dade tana kawo wa dalibai cikas, musamman ma na bangaren Arewacin Najeriya. Ita kanta jarabawar JAMB din, ya kamata a soke ta, a tsaya kawai ga jarabawar WAEC da NECO. Idan dalibi ya ci wadannan, kawai a ba shi gurbin karo karatu a jami’a ko takwararta. Idan ba haka ba, yaranmu na Arewa za su ci gaba da fuskantar matsalar rashin samun guraben karatu, kamar yadda ya kamata. Ba zan manta ba, lokacin da Farfesa Salim ke shugabantar hukumar JAMB, na ji an taba hira da shi, yake cewa akwai shekarar da wata jiha a Kudancin kasar nan ta gabatar da dalibai dubu 29 da suka cancanci shiga jami’a. A lokacin nan, wannan adadi ya wuce fiye da rabin daliban dukkan jihohin Arewa da ke son shiga jami’a. Don haka soke wannan jarabawa ya yi daidai.”
Matakin ya dace amma dai… – Ummillazina Diye-Diye
Bashir Yahuza Malumfashi, a Abuja
Ummillazina Diye-Diye: “Matakin da aka dauka na soke jarabawar Post UTME gaskiya ya dace, amma kuma sai an sanya ido kuma an dauki mataki sosai domin kada su kuma hukumomin jami’o’i da sauran manyan makarantu su rika kawo wa tsarin cikas, ta hanyar son rai wajen daukar dalibai. Cire wannan jarabawa za ta kawo wa dalibai da iyayensu sauki ta fuskar biyan kudaden jarabawa hawa da hawa. Bayan dalibi ya biya kudin WAEC da NECO, ya biya JAMB sannan kuma ya zo ya biya wannan, amma yanzu da aka soke ta, an samu sauki ke nan. Haka kuma, ita kanta JAMB din, yana da kyau a kara inganta tsarinta, a kara mata tsawon kwana, yadda za ta kai shekara uku ko biyar ba ta lalace ba, maimakon yanzu da take lalacewa a shekara daya kawai. Allah Ya sa mu dace, amin.”
Ya yi daidai – Alhaji Abbas
Daga Umar Rayyan
Alhaji Abbas M.Salisu: “Wannan wani abu da dama ya ishe mu, ya dame mu, yana cikin zuciyarmu. Saboda matsala ce da take ci wa duk wani matashi a kasar nan tuwo a karya. Za ka kashe kudi ka yi jarabawar WAEC, ka yi JAMB, in ka ci sannan ka yi ita wannan jarabawa. A gaskiya ina goyon bayan soke ta.”
Na gamsu da soke jarabawar – Alkassim Rabi’u
Daga Umar Rayyan
Alkassim Rabi’u: “A gaskiya ya yi ta wani bangaren, saboda an sauya tsarin da ake gudanar da jarabawar, yanzu ana amfani da tambarin yatsa ne lokacin rubuta JAMB. Don haka ina ganin ita kawai ta isa. Gaskiya ci gaba ne soke wannan jarabawar da aka yi.”