Ko su Obasanjo sun tsorata da warkewar Buhari ne?
Tarihin Cif Olusegun Obasanjo ba boyayye ba ne a wurin ’yan siyasa da masana. Akwai bayanan da suka ce marigayi Janar Murtala Mohammed ma sai da ya koka da halayensa, amma da yake kaddara ta riga fata, shi Obasanjon ne ya gaji Murtala a mulki. Bayan zaben 1979, Obasanjo ya mika mulki ga Shugaba Shehu […]
Tarihin Cif Olusegun Obasanjo ba boyayye ba ne a wurin ’yan siyasa da masana. Akwai bayanan da suka ce marigayi Janar Murtala Mohammed ma sai da ya koka da halayensa, amma da yake kaddara ta riga fata, shi Obasanjon ne ya gaji Murtala a mulki.
Bayan zaben 1979, Obasanjo ya mika mulki ga Shugaba Shehu Shagari, mutane da dama sun ce Obasanjo ya rika kokawa kan barin sa mulki. Da aka yi wa Shugaba Shagari juyin mulki a ranar 31 ga Disambar 1983, Buhari ya zama Shugaban kasa na soja ya jingine tsarin mulki, domin samun halaccin gudanar da mulki irin na soja, an fara kawo canji, amma tafiya ba ta yi nisa ba, kasa da wata 20 aka yi wa Buhari juyin mulki, Janar Ibrahim Babangida ya zama Shugaban kasa. An kawar da Buhari ne a Agustan 1985, bayan ya dauko matakan gyara. Wadanda suka ture shi sai suka raba komai na tattalin arziki suka lalata tsaro da siyasa, aka yi ta samun rikici a kusan ko’ina, kamar rikicin Kafanchan da Zangon Kataf, inda hatta hukuncin da Mai shari’a Karibi Whyte ya yanke kan masu laifi a rikicin sai da Babangida ya soke ya yafe wa wadanda aka yanke wa hukuncin kisa, amma Obasanjo bai ce komai ba.
Aka zo aka karya darajar Naira aka yi ta kare-karen kudin man fetur da kananzir aka rusa matatun man fetur aka sayar da kadarorin gwamnati, aka kassara hukumomin irin su NEPA da NITEL da Kamfanin karafa na Ajaokuta da Kamfanin Taki na kasa (NAFCON) da sauran hukumomin da suke kyautata rayuwar talaka, aka rusa noma da kiwo da sana’o’in hannu, amma Obasanjo bai ce komai ba.
Obasanjo ya fara magana ce lokacin da Janar Sani Abacha ya zama Shugaban kasa ya kafa kwamiti a kan rushewar bankuna da kuma kwamitin Pious Okigbo kan Babban Bankin Najeriya wanda ya bankado satar Dala miliyan 12.2 na rarar man fetur din da aka sayar a lokacin Yakin Tekun Pasha, kuma ganin yana kokarin ganin bayan gwamnati ne Janar Abacha ya kama shi aka yanke masa hukuncin daurin rai-da-rai bayan kotun soja ta same shi da laifin yunkurin juyin mulki, daga baya aka rage hukuncin zuwa daurin shekara 25.
Da Janar Abacha ya rasu, Janar Abdulsalami Abubakar ya zama Shugaban kasa, sai suka hada kai da su Babangida suka yafe wa Obasanjo, suka fito da shi daga kurkuku suka dora shi a kan mulki duk da gargadin da Cif Olu Falae ya yi cewa Obasanjo dan kungiyar asiri ne, inda daga baya ya garzaya kotu kan hakan. Sai kuwa ga shi mun kare da kafuwar Boko Haram a lokacin Obasanjo.
Cif Obasanjo ya aikata laifuffuka 125 da suka wajabta a tsige shi daga mulki, amma maimakon a tsige shi sai ya rika tsige shugabannin Majalisar Dokoki ta kasa, saboda yanayin mutanen da su Babangida suka hada shi da su, wadanda aka raine su tun lokacin da suka yi wa Buhari juyin mulki a 1985, kuma da ya ga ya kafu sosai, sai ya so karya tsarin mulkin kasar nan domin ya yi tazarce karo na uku, kafin ya sha kasa.
Mafi yawanmu mun yi tsammanin da Buhari ya zama Shugaban kasa na farar hula, zai bi sawun duk abubuwan da suka faru ba daidai ba daga 1985 zuwa shekarar 2015. Allah cikin ikonSa sai Buhari ya kamu da rashin lafiya mai tsanani, kuma maimakon wadanda ya amince da su su cika burinsa sai suka ci amanarsa. A nan matsalar take har su Obasanjo da ’yan kungiyarsa da iyayen gidansa suka samu damar batanci ga Buharin.
Alhamdulillahi, yanzu Shugaba Muhammadu Buhari ya samu lafiya da fatan Allah Ya kara masa lafiya da imani nake ba shi shawarar cewa ya fara waiwayar dukan wadanda ya amince musu, amma suka ci amana har makiya suka samu bakin yin magana kafin ya waiwayi masu kokarin ganin bayansa.
Ga alama irin su Obasanjo ba su ji dadin warkewar da Shugaba Buhari ya yi ba ne, shi ya sa suka kaddamar da kungiyoyi da kuma kamfe din kawar da shi a zabe mai zuwa. In ba haka ba, ta yaya za su ce dole Buhari ya kawar da dimbin matsalolin da ya gada a kasa da shekara uku bayan an shafe sama da shekara 30 ana tafka ta’asa?
Buhari fa ya iske kasar nan kusan komai ya tabarbare, an dawo ana neman a samu zaman lafiya ne ma tukuna. Ya samu an sayar da kasar ga ’yan Jari-Hujja, ta yadda hatta mai shara da mai gadi a ma’aikatu da hukumomin gwamnati sai wadannan ’yan Jari-Hujja su kafa kamfanoni a ce sai ta wurinsu za ka samu aiki!
Miyagun shugabannin sun yi babakere a kan dukiyar kasar nan sun kuma rabe ta a tsakaninsu, kasar tana neman durkushewa. Har yanzu ba mu manta rarar kudin da aka samu daga sayar da man fetur ba, lokacin yakin Tekun Fasha har Dala biliyan 12.2 a zamanin Gwamnatin Janar Ibrahim Babanagida, ina aka yi da wadannan kudi. Sannan ina Dala biliyan 16 da aka ce an kashe kan samar da wutar lantarki a zamanin Obasanjo, amma a karshe aka yi gwanjon kamfanin wutar lantarkin ga ’yan Jari-Hujja, mu kuma muka ci gaba da zama a cikin duhu?
Don haka muna kira ga Shugaba Buhari, a shekara daya da watanni da suka saura masa tun yanzu ya dukufa wajen bin kadin barnar da aka tafka daga 1985 zuwa shekarar 2015.
Ya hanzarta kafa kwamiti ko hukuma mai karfin shari’a da za ta kunshi masana da wakilan jama’a na kowane bangare na kasar nan, wadanda aka tabbatar da tsarkinsu a ba su cikakkiyar dama su binciki duk wanda ake zargi da kowane irin laifi da ya shafi tattalin arziki da tsaro da siyasa da komai ma daga sama har kasa.
Yin haka ya zama wajibi a wannan lokaci, kuma zai magance cece-ku-ce da rudu da rudanin da masu laifin suke ta haddasawa a sassan kasar nan. Wajibi ne tun yanzu a bude sabon babi na tsarkake mutane a tsarkake shugabanci ya zamo ana yin komai bisa adalci.
Idan Buhari bai yi wannan gyara ba, ya sani akasarin ’yan Najeriya za su yanke kauna daga ceto Najeriya daga muguwar ta’asar da aka dade ana tafkawa. Eh, dimokuradiyya ake yi da kowane bangaren na majalisa da shari’a da zartarwa ke da rawar takawa, to amma Shugaban kasa ya sani, yana da takalmin karfen da zai take duk wanda ya nemi dankwafar da kasar nan. Idan har ya fahimci akwai mai neman kawo cikas ya rufe ido ya yi amfani da ikonsa ya murkushe shi ya rabu da dogon Turancin da lauyoyi da ’yan boko za su rika yi. Domin mun lura kokarin Buhari na bin doka da oda ya bai wa wadansu damar su ci gaba da aikata ta’asa a karkashin gwamnatinsa. Don haka ya yi amfani da dokar nan da ta ba shi ikon hawa kujerar naki da dokar da ta ba shi cikakken iko wajen zartar da abubuwan da za su zame wa Najeriya alheri ba daidaikun mutane ba.
Alhaji Abdulkarim daiyabu, Shugaban Rundunar Adalci ta Najeriya (MOJIN), Tsohon Shugaban kungiyar ’Yan Kasuwa da Masu Masana’antu da Ma’adanai da Ayyukan Gona ta Jihar Kano, (KACCIMA). Za a iya samunsa ta tarho: 08060116666, 08023106666.