Ko sun mutu suna karya
Wani mutum ne yana noma a gonarsa, sai wata mota ta kwace ta shigo gonar tasa ta bugi itace ta tsaya. Mutanen da ke cikinta su uku ne, kuma ’yan siyasa ne. Nan take manomin nan ya haka rami ya yi musu kabari, ya binne. A lokacin da yake binnewa, daya daga cikinsu ya ce: […]
Wani mutum ne yana noma a gonarsa, sai wata mota ta kwace ta shigo gonar tasa ta bugi itace ta tsaya. Mutanen da ke cikinta su uku ne, kuma ’yan siyasa ne. Nan take manomin nan ya haka rami ya yi musu kabari, ya binne. A lokacin da yake binnewa, daya daga cikinsu ya ce: “Malam ba mutuwa muka yi ba, suma muka yi da sauran ranmu.” Ya yi banza da shi ya binne su. Bayan wani lokaci, da ’yan sanda suka zo, sai ya nuna masu kabarin da ya rufe su, aka ce wane bayani zai yi, sai ya ce: “Su uku ne kuma duk ’yan siyasa ne, na zo binne na karshe ya ce wai suma ya yi bai mutuwa ba, ni kuma sai na gane cewa maganar dan siyasa ba abar yarda ba ce. Sai na ki kula shi, na dauka ko bayan sun mutu ma suna yin karya. Shi ya sanya duk na binne su.”
Daga Shehu Lawali Tsafe 08091573703