Ko taron kasa zai warware matsalolin da suka addabi Najeriya? 4

Wannan it ace matsalar da muka tattauna a Muhawararmu ta wannan makon. Ga yadda muhawarar ta kasance: Ba zai haifar da da mai ido ba -dambatta Malam Umaru Muhammed danbatta: Shirin ya kunshi wata manufa ce daban dake hade da dabarun siyasa da neman biyan bukatar shugaban kasa da ke kan kujerar mulki a zabe […]

Ko taron kasa zai warware matsalolin da suka addabi Najeriya? 4
Ko taron kasa zai warware matsalolin da suka addabi Najeriya? 4

Wannan it ace matsalar da muka tattauna a Muhawararmu ta wannan makon. Ga yadda muhawarar ta kasance:

Ba zai haifar da da mai ido ba -dambatta

Malam Umaru Muhammed danbatta: Shirin ya kunshi wata manufa ce daban dake hade da dabarun siyasa da neman biyan bukatar shugaban kasa da ke kan kujerar mulki a zabe mai zuwa na 2015.
Idan Shi Shugaban kasa ya manta mutanen Najeriya masu aiki da hankalin da Allah ya ba su ba su manta ba game da batun shirin da aka taba aiwatar na cewa wadannan wakilan su je su bi mazabunsu, domin jin ra’ayoyin jama’arsu game da hanyar da za’a bi domin warware matsalolin da kasarnan take fama na bangaren shugabanci da sauran haka to wani sakamako suka mika wa kwamitinsu? Don haka wannan za a gane babu gaskiya a wannan shirin ballantana a yi tsammanin warware ko kawo karshen matsalolin kasan nan.