Ko taron kasa zai warware matsalolin da suka addabi Najeriya? 5

Wannan it ace matsalar da muka tattauna a Muhawararmu ta wannan makon. Ga yadda muhawarar ta kasance: Babu maslaha da wannan taron zai kawo wa kasar nan – Alhaji Bello A ganina ni Alhaji Bello.M.Sagera ko kadan banda cutar da jama’ar kasa domin wata hanya ce ta neman cin kudi da neman dorewa akan shugabanci […]

Ko taron kasa zai warware matsalolin da suka addabi Najeriya? 5
Ko taron kasa zai warware matsalolin da suka addabi Najeriya? 5

Wannan it ace matsalar da muka tattauna a Muhawararmu ta wannan makon. Ga yadda muhawarar ta kasance:

Babu maslaha da wannan taron zai kawo wa kasar nan – Alhaji Bello

A ganina ni Alhaji Bello.M.Sagera ko kadan banda cutar da jama’ar kasa domin wata hanya ce ta neman cin kudi da neman dorewa akan shugabanci na tazarce da dabara irin na Goodluck da abokan shawararsa masu son gina kansu su ha’inci alumman kasa. Dalili kuwa ai an taba yin irin wannan taron ba sau daya ba, kuma hakan batun ya shiririce don haka matsalar Najeriya matsala ce da ta shafi rashin shugabanci na kwarai kuma abin da za a duba ai kasar nan akwai tsarin mulki amma abinda yake faruwa shi ne  ba’a yin aiki da shi domin amfanin jama’a.