Ko taron Musulmin duniya da aka gudanar a Abuja zai kawo hadin kan Musulmi a Najeriya?

A makon da ya gabata ne kungiyar Izalatul Bid’a Wa’ikamatus Sunna ta shirya wani gagarumin taron Musulmi na duniya, wanda ya tattara mahalarta daga akidoji daban-daban na Musulunci. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko wannan taron zai iya kawo hadin kan al’ummar Musulmi a Najeriya. Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga […]

Ko taron Musulmin duniya da aka gudanar a Abuja zai kawo hadin kan Musulmi a Najeriya?
Ko taron Musulmin duniya da aka gudanar a Abuja zai kawo hadin kan Musulmi a Najeriya?

A makon da ya gabata ne kungiyar Izalatul Bid’a Wa’ikamatus Sunna ta shirya wani gagarumin taron Musulmi na duniya, wanda ya tattara mahalarta daga akidoji daban-daban na Musulunci. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko wannan taron zai iya kawo hadin kan al’ummar Musulmi a Najeriya. Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa:

Taron zai iya kawo hadin kai – Malam Yahuza

Malam Yahuza Lawal Ladan: “Wannan taro da aka gudanar a Abuja, babu shakka zai iya kawo hadin kan al’ummar Musulmi a Najeriya, musamman idan muka yi la’akari da cewa taron ya hada al’umma daga kasashen duniya, ba wai kasashen Afirika kadai ba. Haka kuma an samu haduwar malamai na bangarorin akidu daban-daban. A wurin taron ne ma Malam Bello Yabo ya bayyana mamakinsa, cewa bai taba zaton za a iya gudanar da irin wannan taron ba. Hakan ke nuna cewa lallai an samu nasara, tun da aka sha inuwa daya tsakanin manyan malamai, masu mabambantan akidoji. Don haka, yanzu sai al’umma su yi kokarin maida hankali wajen bautar Allah da gaskiya tare da neman ilmi, kuma mu ci gaba da nuna wa juna kauna, bisa ’yan uwantakatar Musulunci.”

Za a yi nasarar hada kai idan…- Malam Abdulrahman

Malam Abdulrahman BKK: “A ra’ayina, ganin yadda aka gudanar da wannan babban taro kuma aka fadakar da al’ummar Musulmi da wa’azoji masu ratsa zukata, za a iya samun nasarar hadin kan Musulmi a kasar nan, musamman idan al’umma suka yi aiki da wa’azojin da suka saurara. Idan kowa ya ajiye son ransa gefe guda, aka koma ga Allah bilhakki da gaskiya, za a samu hadin kan Musulmi. Za a samu fa’ida idan kowa ya yi hukunci da littafin Allah da sunnar Manzon Allah (saw). Amma idan bayan wannan taron, muka koma kan ayyukanmu da halayenmu na son rai, yana da wuya a ce za a samu canjin al’amura kuma hakan zai sanya a samu matsala wajen hadin kan Musulmi. Don haka ina ba mu shawara da mu yi aiki da wa’azojin da muka saurara daga bakunan malamai na garskiya, mu bauta wa Allah bisa hujja kamar yadda Ya umurta. Allah Ya sa mu dace, amin.”

Hadin kai zai iya samuwa – Abdullahi Alkwatonawi

Malam Abdullahi Alkwatonawi: “Eh, a gaskiya za a iya samun hadin kan da a ke fata a tsakanin Musulmi, duk da yake cewa kowace kungiya tana da tata akidar, hadin  kan zai samu ne kawai in an bar kowace kungiyar da tata akidar; aka kuma hadu a kan manufa guda, wato Musulunci.”

Taron alama ce ta hadin kai – Muhammadu Namadi

Malam Muhammadu Namadi: “Na samu halartar taron kuma ganin yadda ya hado shuwagabannin kungiyoyi daban-daban, hakan ’yar manuniya ce na samuwar hadin kai a tsakanin Musulmin kasar nan; domin ko a nan aka tsaya an samu hadin kan. Domin an hadu gaba daya a taron, an kuma gabatar da kasidu da jawabai iri-iri, kuma daman mu  ’yan Izala da ’yan darika, Musuluncinmu iri daya ne, duk yardarmu guda ce, fahimtarmu ce kawai ta bambanta mu.”

Zai kawo hadin kai idan… – Muhammad Inuwa

Muhammad Inuwa Ado: “Ni a nawa ganin, wannan taro na Izala zai iya kawo hadin kan al’ummar Musulmi amma fa sai an yi amfani da fadin Allah da manzonSa. Amma muddin aka kauce wa fadin Allah, ya zama an yi taro ne don son zuciya da neman duniya, babu yadda za a yi a samu biyan bukata na hade kan al’ummar Musulmi waje guda. Wani lokaci maganar da ake fada a bainar jama’a ba ita ce har zuciya ba, shi ya sa ake samun matsala.”

Zai kawo hadin kan Musulmi waje guda – Sani Keeto

Sani Keeto Gombe: “Lallai wannan taro da kungiyar Izala ta kira, zai yi tasiri domin shi ne irinsa na farko a duniya, wanda kuma an yi shi ne domin hadin kan jama’ar Musulmi baki daya. A nawa bangaren, ina mai yaba wa kungiyar Izala da wannan kokari nata, domin ta gayyato sauran kungiyoyi irin su darikar Tijjaniya da kadiriyya da ma ’yan uwa wadanda ba Musulmi ba, domin su ba da gudunmawarsu wajen ganin an hada kan. Ina mai ba da shawara wajen ganin an ci gaba da gudanar da irin wannan taro lokaci-lokaci don kar a shagala wajen aibanta juna hakan kuma zai kawo hadin kai kwarai da gaske.”