Ko tsarin bangayen littattafan Hausa sun dace?

Na yanke shawarar yin wannan rubutu ne domin ba da gudunmowa, ta wajen kawo gyara don ciyar da rubutu gaba; ganin yadda adabin zamani ke ta tangal-tangal, musamman ma dai rubutu.Wannan karon na dauki wannan bangare ne na bangon littafi, domin ganin yadda yake ta tabarbarewa a mafi yawancin littattafanmu na Hausa. Wala alla idan […]

Ko tsarin bangayen littattafan Hausa sun dace?

Na yanke shawarar yin wannan rubutu ne domin ba da gudunmowa, ta wajen kawo gyara don ciyar da rubutu gaba; ganin yadda adabin zamani ke ta tangal-tangal, musamman ma dai rubutu.
Wannan karon na dauki wannan bangare ne na bangon littafi, domin ganin yadda yake ta tabarbarewa a mafi yawancin littattafanmu na Hausa. Wala alla idan aka yi dace sai a samu gyara, wanda shi ne fatanmu a kodayaushe.
To, da farko dai zai kyautu mu fahimci ma shi kansa bangon, manufar yinsa, tsari da kuma bambancin namu tsarin da wanda duniya ta yarda da shi.
Bangon littafi ya kyautu ya zamana mai karfi da aminci domin killace takardun ciki, wadanda su ne ma littafin; domin tun daga nan mai karatu zai fara zaton karanta abin arziki. Sannan kalmomin da yake dauke da su, wadanda suke nuni da abin da littafin ya kunsa, su ma akan kambama su cikin sassaukan tsari da launi, domin su ja hankalin mai saye ko mai karatu.
Sannan akwai launi ko kalar bangon, ya kyautu su dinga amsa abin da littafin ke dauke da shi. A misali, idan za a yi littafin yaki, kaloli masu zafi kamar ja da dorawa da giftawar baki za su fi dacewa da jigon littafin. Idan kuma littafi ne na soyayya, to sai a sarrafa kore da shudi da fari da dan ja, don ya wakilci zuciya. Fari a matsayin aminci, kore kuma dama mun san kala ce mai sanyaya rai. Duk inda ka ga ja, to dama tana wakiltar zuciya ne. Kai da ma sauran kaloli barjik. Ka ga ba a yi littafin yara a dauki baki ko ja a maka ba, sai irinsu kalar algashi, dorawa bula kore da sauransu.

Ba su cika ka’idojin dab’i
Bayan haka, akwai alama da akan yi, wadda take dada jaddada abin da aka rubuta, wanda a Turance ake kira (Illustration).Wannan ya kunshi hotunan abubuwa da dama, wadanda ana ganinsu za a fahimci inda littafin ya sa gaba.
To, a nan ne fa gizo yake sakar, domin idan muka binciki littattafanmu na Hausa, za mu ga da yawa sakon cikin littafi daban, alamar bango da ke bangonsa ma daban. Wato, abin takaicin ma shi ne, wai sai ka ga an yanko hoton Baturiya ko indiya an makala mata dankwali, wai da sunan littafin Hausa. Za ka ga koda labarin mummuna ake so a bayar, to bangon sai an sa masa hoton kyakkyawa.
Na taba hira da wani dan kungiyar marubuta a kan wannan batu, sai yake cewa wai idan ba haka aka yi ba, ba a sayen littafin. Ni kuma na ce to ashe in dai bango zai zamo haka, to abin cikin ma haka yake ke nan. Kuma shin haka marubuci zai zauna, sai abin da mutane suke so zai yi? To, lallai kuwa in dai haka ne, ashe mutane ne suke juya marubuci, ba shi yake juya su ba. Wannan fa shi ne reshe ya yuye da mujiya! Ba haka kuma ya kamata abin ya kasance ba. Marubuci ya kamata ya gabatar wa makarantansa sabbin kudurori, manufofi da bayanan da za su sauya su daga gurbatattu zuwa nagari.

Abin da ake la’akari wajen suka
Da yawa daga cikin masu sukar littattafan Hausa, suna la’akari ne da abin da suke gani a bangayen littattafan, domin yawanci ba karatun suke ba. Kowa dai ya ga ‘yarsa ta dauki littafi, dauke da hotan budurwa, ya san ba zai wuce soyayya ba. Kuma na yi imanin da yawa akwai abin da al’umma za su karu da shi, amma rashin kyakkyawan tsari ya sa ana yi wa littattafan kallon uku-kwabo-biyu-ahu.
Ka takarkare ka zabga rubutu kuma da kanka ka binne shi, wannan kwaba har ina! Domin ba a ce rashin basira ba.
Ina tabbatar mana da cewa, da za mu yi wa juna fada a kungiyance, a kawo wani tsari da zai inganta tsarin bugu da wallafar littattafanmu, to nan da ’yan shekaru za mu yi mamakin canjin da za a samu a cikin al’ummarmu.
A yanzu littafin da ya fi kowanne kasuwa a duniya ma ko hoto babu a tare da shi, kuma da yawa haka suke a ko’ina. Mu ne dai da ka dauki littafinmu sai ka ga yana yi maka kama da tatsuniya. Da kanmu mun maida littattafanmu sun zama na yara. Mu duba makwaftanmu mana na Kudu. Ai ba haka kawai suka wuce mu ba, kuma ba don sun fi mu abin fada ba ne. Ko kusa, kodayaushe mu ake kallo da rashin gudanar da abubuwa cikin tsari. Kowa yana ganin shi gagararre ne.
Bangon littafin Ruxanin TunaniMisali, a ilimance idan aka kira littafi da suna, ‘Kishi Kumallon Mata’ ai ba lallai ba ne sai ka nuna hotan mace ba. Idan ka dauki kaloli biyu masu kyau da ba su jituwa a ido, za su fi ba da ma’ana. Ita dai harkar rubutu sadaukarwa ce kawai da rufin asiri, ba kudi ake tarawa da ita ba. Mu duba tarihin wanda ya fi kowa sayar da kwafin littafi a duniya, mu ga na nawa ne shi a masu kudin duniya?

Abin da ake bukata
Lallai muna bukatar sake tunani ta fuskar tsara bangayen littattafanmu, domin su dace da ka’idojin wallafa a duniya baki daya, kuma domin su kawo mana fa’idar karatu da rubutu a cikin al’ummarmu. Wannan ne zai iya tabbatar mana da dacewa da manufar rubutu da wallafa. Allah Ya sanya mu dace, amin!
Bashir ya rubuto wannan sharhi ne daga birnin Kuala Lumpur na kasar Malesiya, inda yake karatu.