Ko ya dace a amince fursunoni su rika amfani da wayar hannu?

Duk wanda aka ce an yanke masa hukuncin zama a gidan yari, hakan na nufin an dakile masa ’yancin walwala, musamman tafiya daga nan zuwa can har sai adadin ya kare. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko ya dace a amince wa fursunoni su rika amfani da wayar hannu a yayin da suke […]

Ko ya dace a amince fursunoni su rika amfani da wayar hannu?
Ko ya dace a amince fursunoni su rika amfani da wayar hannu?

Duk wanda aka ce an yanke masa hukuncin zama a gidan yari, hakan na nufin an dakile masa ’yancin walwala, musamman tafiya daga nan zuwa can har sai adadin ya kare. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko ya dace a amince wa fursunoni su rika amfani da wayar hannu a yayin da suke tsare a wakafi? Ga abin da wakilanmu suka kalato mana:

Bai dace a yi haka ba – Abdullahi Bindawa

Ahmad Kabir, a Katsina

Abdullahi Bindawa: “A’a, bai dace mai laifi yana amsa waya ba sai don in abin ya zamo dole saboda juyin zamani, shi ma ya zamo yana tare da ma’aikaci kuma ana jin abin da suke magana. Yin wayar yana iya jawo cutuwa kodai ga wurin tsaron koma yankin baki daya. Kuma zafin hukuncin da ake so ya ji tamkar ba a yi ba tunda ya nuna yana walwala saboda waya a yanzu ta zamo wani sashi na jin dadin rayuwa saboda mafi yawan al’amurran wannan lokacin suna gudana ne ta amfani da ita.”

Barin su da waya kasada ce – Musa Otega

Sani Gazas Chinade, a Damaturu

Malam Musa Otega: “Dangane da cewar a bar fursunoni su mallaki wayar salula shi ya fi ko akasin hakan, a gaskiya barin su su mallaki wayar salula babbar kasada ce. Dalilina na fadar haka kuwa shi ne, mallakar wayar salula ga fursunoni kan iya ba su damar magana da abokan burminsu ta yadda za su iya gudanar da abin da suke so ta hanyar waya. Don haka rike wayar hannu ga ’yan zaman jarun ba ta da wani alfanu illa ma ta kara haddasa miyagun abubuwa.”

Ban goyi bayan haka ba – Muhammad Shafi’i

Ahmad Kabir, a Katsina

Muhammad Shafi’i Yahaya: “Bai kamata a bar fursuna ya rika amfani da wayar hannu ba a cikin gidan wakafi. Saboda wadanda ba gaskiya ta kai su gidan ba za su iya dorewa da wannan rashin gaskiyar ta wannan hanya. Ita wannan hanyar sadarwa a wani sashen tana bayar da gudunmuwa a yanzu a wajen harkar ta’addanci. Har’ila yau, wanda aka tsare din an yi haka ne domin ya yi ladabi, to barinsa ya zamo tamkar ba a yi masa komai ba ke nan.”

Bai kamata ba – Adamu Maidawaki

A.A. Masagala, a Benin

Adamu Maidawaki: “A zahiri idan har gaskiya ake yi wa aiki, lallai bai dace ba a ce wanda aka kama shi da laifi har ya kai aka tusa keyarsa zuwa gidan yari sannan a ce an bar shi yana amfani da wayar sadarwa ba, ko da wasa wannan babban kuskure ne da zai cutar da kasa har da ita hukumar kanta. Dalilina shi ne, yau fa a kasar nan muna da kungiyar sari-ka-noke da take ikirarin kafa wata daular isgilance, wadda a yanzu haka gwamnati take fafatawa da ita kuma mai yiwuwa da ’ya’yan wannan kungiyar a wasu gidajen yarin kasar nan. Don haka ina ganin muddin ana barin masu laifi da suke tsare a gidan yari suna amfani da wayar tafi da gidanka to lallai wannan damar da suka samu ba za ta haifar da da mai idoba, domin da wannan za su iya kulla duk wani sharri na kawo cikas da hana zartar da hukunci a kansu. Kuma ina ganin hakan babbar fallasa ce ga gidajen yarin kasa kuma zai iya a nan gaba ya hana masu manyan laifi wadanda suke tsare a gidajen yarin su yi da’a ga kotunan kasa kuma ya nuna da alama babu wata doka ta ladabtarwa ga masu aikata laifi a kasa.”

Hakan zai yi illa – Balarabe Maitakalma

Sani Gazas Chinade, a Damaturu

Balarabe Maitakalma: “A ganina dangane da cewar ko a bar fursunoni su rika amfani da wayar salula, wannan magana ce kawai da ba za ta haifar wa al’umma da mai ido ba. Dalilina na fadar haka kuwa shi ne, yaya za a ce mai laifi kuma a bar shi ya rike wayar hannu? Ai hakan ba da dama ne ga dan zaman jarun ya samu damar ci gaba da ba da umarni kan ayyukansu duk da cewar ba duk ’yan zaman fursuna suke masu munanan halayya ba, domin akwai kaddara. Don haka akwai bukatar yin hattara dangane da wannan lamari na barin ’yan fursuna su mallaki wayar hannu.”

Bai dace ba – Tanko Lokoja

A.A. Masagala, a Benin

Alhaji Tanko Lokoja: “A hakikanin gaskiya, ina ganin barin mai laifi da ke tsare agidan wakafi da ko wace na’ura ma bai dace ba bellantana wayar salula. Wannan yana nuna tamkar an kashe maciji ne ba a yanke kansa ba. Dalilina shi ne, duk wanda yake tsare a gidan wakafi muddin ya samu irin wannan damar ba mamaki ta hanyar da ya samu wannan dammar, yana iya ya kulla wani makirci da wasu miyagu daga waje. Kun ga abin da ake gudun ba a tsira ba.
“Saboda haka barin wanda yake tsare a gidan yari da wayar sadarwa babban hadari ne ga kasa. Idan aka yi la’akari da irin ayyukan na wasu kungiyoyin a wasu lokutan game da yadda suke yi wa gidajen yari dirar mikiya, su bude su fitar da ’yan uwansu masu manyan laifi. Don haka ina ganin ya kamata hukuma ta dauki matakin hana fursunoni rike wayar salula komai matsayin mutum idan yana gidan yari a tsare.”