Ko ya dace a ba mutum mukami ba tare da an tuntube shi ba?

An samu tabbacin cewa a matakin gwamnatin jiha da ta tarayya, ana nada wasu mutane mukamai, kamar Kwamishina ko Minista ba tare da an tuntube shi ba. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko ya dace a rika yin haka, ko kuwa a rika tuntubar mutum a ji ra’ayinsa kafin a nada shi? Ga […]

Ko ya dace a ba mutum mukami ba tare da an tuntube shi ba?
Ko ya dace a ba mutum mukami ba tare da an tuntube shi ba?

An samu tabbacin cewa a matakin gwamnatin jiha da ta tarayya, ana nada wasu mutane mukamai, kamar Kwamishina ko Minista ba tare da an tuntube shi ba. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko ya dace a rika yin haka, ko kuwa a rika tuntubar mutum a ji ra’ayinsa kafin a nada shi? Ga abin da wasu mabambantan mutane suka bayyana:

Rashin sanarwa ya fi dacewa – Alhaji Bala

Hamza Aliyu, a Bauchi

Alhaji Bala Mai’auduga: “Kamar yadda kowa ya sani ne, a Najeriya akwai wasu da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba su mukamai a sassa daban-daban, alhali ba su da masaniyar cewa za su samu wannan mukami. Saboda haka a ra’ayina, ina goyon bayan a ba mutum mukami ba tare da an tuntube shi ba, hakan shi ya fi dacewa. Koda alheri ne za ka yi wa mutum, ya fi dadi ka ba shi ba tare da ka sanar da shi ba.
“Duk wanda aka ba shi mukami a babin ya cancanta, to tabbas zai yi abin da ya kamata; domin dama ba shi ya nema ba. Idan ka duba a bisa tsarin addinin Musulunci, an ce duk wanda ya ce a ba shi mukami, kada ku ba shi; a dubi wanda ya cancanta a nada, domin shi ne zai yi abin da ya kamata ga al’umma. Daga karshe ina ganin babu dalilin da zai sa mutum a ba shi mukami ya ki karba saboda wai ba a sanar da shi ba.”

Ya dace a ba shi ba tare da tuntuba ba – Dauda Udubo

Hamza Aliyu, a Bauchi

Alhaji Adamu Dauda Udubo: “Tabbas kamar yadda kowa ya sani ne, wasu lokutan ana ba da mukamai ga wasu daga cikin ’yan Najeriya da ake ganin sun ba da gudunmawa ba tare da an sanar da su cewa za a ba su mukami ba. A fahimtata, wannan mataki ya dace sosai, domin duk wanda ya rike gaskiya da rikon amana a rayuwa, Allah ba Ya hana shi abin da zai ci. Halayen mutum na gaskiya da kamanta adalci su suke nuna shi ga mutanen duniya har a yi masa shaida tagari a tsakanin al’umma.
“Akwai wasu daga cikin mutane masu ra’ayin rikau, za ka ji an ba su mukami a matakin gwamnatin jiha ko ta tarayya amma kafin su karba sai sun gindaya wasu sharuda. Misali, Shugabanmu na yanzu, Muhammadu Buhari; lokacin da za a ba shi shugabancin PTF, kafin ya karba sai da ya sa wasu sharudda ga gwamnati. ’Yan kasa ne suka ce Muhammadu Buhari ya zo ya rike musu mukamin Shugaban kasa saboda haka ba na goyon bayan a sanar da mutum kafin a ba shi.”

Bai dace ba komai cancantarsa – Haruna Aliyu

Abubakar Haruna, a Abuja

Haruna Aliyu: “Gaskiya bai dace a bai wa mutum mukami ba tare an tuntube shi ba komai iliminsa da cancantarsa saboda kila a wannan lokacin a tunaninsa akwai abin da yake son ya yi ko kuma yana da wani uzuri mai karfi da zai hana shi rike mukaminsa, kamar na rashin lafiya da makamancin haka.”

Ya dace idan an amince da shi – Muhammadu Umar

Abubakar Haruna, a Abuja

Muhammad Umar: “Ya dace a bai wa mutum mukami ba tare da an tuntube shi ba, muddin idan aka amince da mutum zai iya rike mukamin ba tare da wata matsala ba saboda gasiyarsa da nagartarsa da kwarewarsa da kuma rikon amanarsa.”

Ba sai an tuntubi mutum – Asabe Tirwun

Hamza Aliyu, a Bauchi

Hajiya Asabe Isa Tirwun: “Abin da zan fada game da wannan tambaya shi ne, a kasar nan yanzu mulkin demokuradiyya muke yi saboda haka yanzu an bar kiwon dabbobi kiwon mutum ake yi; kowa mutane suna kallon yadda yake tafiyar da harkokin rayuwarsa. Don haka a ra’ayina, idan gwamnati za ta ba mutum wani mukami ba sai ta tuntube shi ba. Cancantar mutum yakan sa a ba ka mukamin da idan kai ne ka nema ba za ka samu ba. Misali, sarautar gargajiya da ake gadonta, za ka ga wasu sun fito suna nema amma masu zaben sarki sai su dauko wani daban, wanda ba ya daga cikin masu nema domin suna ganin ya cancanci ya shugabanci al’umma.
“Shugabanci na Allah ne, Yakan bayar ga wanda ya so a kuma lokacin da ya ga dama duk wanda za a ba shi mukami a ba shi kawai, ba tare da sai an tuntube shi ba. Akwai abin da za ka iya, akwai kuma mukamin da ko an ba mutum ba zai karba ba, domin ya san cewa mukamin ya fi karfinsa.”

Babu dalilin sanarwa kafin… – Dokta Adama

Hamza Aliyu, a Bauchi

Dokta Adama Garba Gadi: Abin da zan fada game da wannan tambaya shi ne, ba na goyon bayan a sanar da mutum kafin a ba shi wani mukami a gwamnatance domin duk wanda yake zaune lafiya da al’umma shi ne ya kamata a ba shi mukami. Idan ka duba Shugaban kasa Muhammadu Buhari, akwai wasu daga cikin wadanda ya ba su mukamin minista, akwai wadanda a jaridu suka ga sunayensu cewa za a ba su mukami. Akwai mata biyar daga cikin wadanda aka ba su mukamin minista, da yawa daga cikinsu babu wacce ta tsammaci ce wa za ta samu wannan babban mukami.
“Kafin Gwamna ko Shugaban kasa ya ba mutum wani mukami na siyasa sai da aka gudanar da muhawara a sirrance kowa an san irin gudunmawar da ya bayar daidai bakin gwargwado. Saboda haka a ra’ayina babu wani dalili da zai sa sai an sanar da mutum kafin a ba shi mukami.”