Ko ya dace a biya shugabannin Majalisun Tarayya fansho har bayan rai? 1
A yayin da ake yi wa Kundin Tsarin Mulki kwaskwarima, akwai yiwuwar amincewa da dokar da za ta tabbatar da a rika biyan shugabannin Majalisun Tarayya fansho bayan sun sauka daga mulki har zuwa mutuwarsu. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a rika biyansu irin wannan kudi? Wakilanmu sun tattauna da mabambantan […]
A yayin da ake yi wa Kundin Tsarin Mulki kwaskwarima, akwai yiwuwar amincewa da dokar da za ta tabbatar da a rika biyan shugabannin Majalisun Tarayya fansho bayan sun sauka daga mulki har zuwa mutuwarsu. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a rika biyansu irin wannan kudi? Wakilanmu sun tattauna da mabambantan mutane kuma ga ra’ayoyinsu kamar haka:
Gara ma a kula da ma’aikatan gwamnati – Fatima Sulaiman
Fatimah Sulaiman Borgu: “Bai kamata su ci wannan moriyar da ake kokarin yi musu tanadi a kai ba, musamman da ake maganar har sai sun mutu sannan ya tsaya. Wannan rashin adalcin har ina! Ai ba ta wadannan ya kamata a sa a gaba ba, ya kamata a bi ma’aikatan gwamnati wadanda suka bar aiki bayan an tilasta musu shiga cikin shirin adashin fansho, a ji yaya suke fama da rayuwar yau da kullum? Wadannan mutanen da ake magana ba talakawa ba ne, musamman irin mukaman da za a ba su a fakaice har sai sun ce ba su so.”