Ko ya dace a biya shugabannin Majalisun Tarayya fansho har bayan rai? 2
A yayin da ake yi wa Kundin Tsarin Mulki kwaskwarima, akwai yiwuwar amincewa da dokar da za ta tabbatar da a rika biyan shugabannin Majalisun Tarayya fansho bayan sun sauka daga mulki har zuwa mutuwarsu. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a rika biyansu irin wannan kudi? Wakilanmu sun tattauna da mabambantan […]
A yayin da ake yi wa Kundin Tsarin Mulki kwaskwarima, akwai yiwuwar amincewa da dokar da za ta tabbatar da a rika biyan shugabannin Majalisun Tarayya fansho bayan sun sauka daga mulki har zuwa mutuwarsu. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a rika biyansu irin wannan kudi? Wakilanmu sun tattauna da mabambantan mutane kuma ga ra’ayoyinsu kamar haka:
Wannan doka son zuciya ne a sarari – Dokta Baninge
Dokta Ibrahim Baninge: ‘’A ra’ayina, wannan doka da ake son a fitar ta a rika biyan shugabannin Majalisun Tarayya kudaden fansho har karshen rayuwarsu bai da ce ba kuma son zuciya ne a sarari. Domin ba a dubi mutanen Najeriya da suka yi zabe ba, wajen tunanin cewa za a kafa wannan doka. Mutanen Najeriya da suka yi zabe, ba wannan ne damuwarsu ba, damuwarsu ita ce a fitar masu da dokokin da za su inganta rayuwarsu, ta hanyar samar masu da tsaro da hanyoyin mota da ilmi da wutar lantarki da inganta harkokin noma da dai sauransu. Su yi hakuri da irin makudan kudaden da suke karba a lokacin da suke kan kujera. Su rika dokokin da za su taimaki al’ummar kasa. Kada su ce zasu rika yin dokokin da za su amfane su kadai.”