Ko ya dace a biya shugabannin Majalisun Tarayya fansho har bayan rai? 3

A yayin da ake yi wa Kundin Tsarin Mulki kwaskwarima, akwai yiwuwar amincewa da dokar da za ta tabbatar da a rika biyan shugabannin Majalisun Tarayya fansho bayan sun sauka daga mulki har zuwa mutuwarsu. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a rika biyansu irin wannan kudi? Wakilanmu sun tattauna da mabambantan […]

Ko ya dace a biya shugabannin Majalisun Tarayya fansho har bayan rai? 3
Ko ya dace a biya shugabannin Majalisun Tarayya fansho har bayan rai? 3

A yayin da ake yi wa Kundin Tsarin Mulki kwaskwarima, akwai yiwuwar amincewa da dokar da za ta tabbatar da a rika biyan shugabannin Majalisun Tarayya fansho bayan sun sauka daga mulki har zuwa mutuwarsu. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a rika biyansu irin wannan kudi? Wakilanmu sun tattauna da mabambantan mutane kuma ga ra’ayoyinsu kamar haka:

Lokaci bai yi ba na wannan doka – Umar Ahmad

Umar Ahmad: “A gaskiya lokaci bai yi ba da za a yi wa wadannan Shugabannin shirin wannan garabasar fanshon har sai rai ya yi halinsa. Magana ta gaskiya, da dama daga cikin ’yan Najeriya na fama da fatarar da b  su da tabbacin samun abun kai wa bakinsu a kulluyaumin. Mutanen da ake magana kansu, fanshon ma ba za su damu da shi ba don kuwa suna da harkokinsu da suke gudanarwa, wadanda suke samun na rufin asiri su da iyalinsu. karamin misali, ka gaya mini daya daga cikin wadanda suka taba rike wannan kujerar da a halin yanzu ya zama abin tausayi.”

Matsalar Tsaro: Dole mu faɗakar da mutane yadda za su kare kansu – ACF

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna