Ko ya dace a biya shugabannin Majalisun Tarayya fansho har bayan rai? 5
A yayin da ake yi wa Kundin Tsarin Mulki kwaskwarima, akwai yiwuwar amincewa da dokar da za ta tabbatar da a rika biyan shugabannin Majalisun Tarayya fansho bayan sun sauka daga mulki har zuwa mutuwarsu. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a rika biyansu irin wannan kudi? Wakilanmu sun tattauna da mabambantan […]
A yayin da ake yi wa Kundin Tsarin Mulki kwaskwarima, akwai yiwuwar amincewa da dokar da za ta tabbatar da a rika biyan shugabannin Majalisun Tarayya fansho bayan sun sauka daga mulki har zuwa mutuwarsu. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a rika biyansu irin wannan kudi? Wakilanmu sun tattauna da mabambantan mutane kuma ga ra’ayoyinsu kamar haka:
Kafa wannan doka bai dace ba – Habibu Abubakar
Alhaji Habibu Abubakar: ‘’A gaskiya a tunanina kafa wannan doka ta bai wa shugabannin Majalisun Tarayya fansho har karshen rayuwarsu bai dace ba, domin a kullum wadannan shugabannin majalisu ba su da wani tanadi da suke yi don talakan kasar nan ya sami yadda zai ci abinci sau uku a rana. A kullum tunaninsu shi ne yaya za su yi su inganta rayuwarsu da ta iyalansu. Kaso mafi tsoka na kasafin kudin kasar nan yana tafiya wajensu ne. Don haka mene ne kuma suke nema da za su ce za su kafa wannan doka? Don haka kafa wannan doka bai dace ba. Damuwar talakan kasar nan shi ne rashin kwanciyar hankali da talauci. Don haka dokokin da ’yan majalisa ya kamata s uyi ke nan kan magance wadannan matsaloli.”