Ko ya dace a bude kofofin iyakar kasa domin shigo da shinkafa?
A kwanaki ne mai marbata Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar da Gwamnan Sakkwato, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal suka yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta bude kofofin iyakar Najeriya na kasa, domin a samu saukin shigowa da shinkafa da nufin saukaka tsadarta a cikin gida. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a […]
A kwanaki ne mai marbata Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar da Gwamnan Sakkwato, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal suka yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta bude kofofin iyakar Najeriya na kasa, domin a samu saukin shigowa da shinkafa da nufin saukaka tsadarta a cikin gida. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a bude hanyoyin? Wakilanmu sun kalato ra’ayoyin jama’a, kamar haka:
Bai dace a bude
kofofin ba – Sabo Muhammad
Bashir Yahuza Malumfashi, a Abuja
Malam Sabo Muhammad: “Ni dai a ra’ayina, bai dace a sake bude hanyoyin shigowa Najeriya da nufin shigo da shinkafa ba. Dalili kuwa shi ne, ita gwamnati ta rufe hanyoyin ne da nufin ’yan kasa su dogara da kansu wajen samar da kayan abincin da zai wadace su. Idan har muka dogara da kanmu ta fuskar noma, wannan zai sanya ’yan kasa su rage dogaro da gwamnati kuma hakan zai rage zaman banza da matasa suke yi, domin kuwa za a samu ayyukan yi da sana’o’i. Idan mun duba, a can baya ai da noma kasar nan ta dogara kuma da shi ne aka samu kudin hako fetur. Don haka rufe hanyoyin zai ba mu karfin gwiwar komawa noma da kiwo, domin wadata kasa da abinci, sannan zai magance ayyukan ta’addanci, zai magance zaman banza. Don haka bai kamata a sake bude hanyoyin shigowa Najeriya na kasa ba.”
Bai kamata a bude kofofin ba – Zubairu Muhammad
Bashir Yahuza Malumfashi, a Abuja
Zubairu Muhammad: “Kamar yadda nake gani, bai dace a bude hanyoyin kasar nan da nufin wai a samu saukin shigo da kayan abinci ba. Dalilina na fadin haka shi ne, domin tun da farko, an kulle su ne da nufin daukar matakan tsaro kan ’yan ta’adda, masu shigowa domin yin barna ga al’ummar kasa. An dauki matakin ne ba domin takura wa talakawa ba, an yi haka ne da nufin dakile ’yan Boko Haram. Shi Sarkin Musulmi, kamata ya yi a ce ya yi magana kan wasu abubuwan masu muhimmanci, amma ba game da wannan ba, domin kuwa rufe hanyoyin kasa bai hana ’yan kasuwa su shigo da shinkafa ta hanyoyin ruwa ba. Duk dan kasuwar da ke son shigo da shinkafa, zai iya shigo da ita ta hanyar ruwa, idan ya biya harajin ka’ida. Kuma wannan mataki zai bunkasa noma a Najeriya, domin hakan zai ba manoman cikin gida damar noma abincin da zai wadace mu kuma su samu kudin shiga mai yawa. Don haka bai kamata a bude hanyoyin ba, domin hakan zai taimaki kasa ne.”
Ya dace a bude kofofin – Ya’u Bala Jingir
Hussaini Isah, a Jos
Alhaji Ya’u Bala Jingir: ‘’Ya kamata kafin gwamnati ta rufe kan iyakar kasar nan wajen shigo da shinkafa a ce muna da shinkafar da ta wadace mu. Amma yanzu shinkafar da muke nomawa a kasar nan ba ta wadatar da mu. Don haka idan aka ce a daina shigo da shinkafa zuwa kasar nan a yanzu akwai matsala. Hana shigo da shinkafar nan ne ya sanya farashin wasu abubuwa da dama sun tashi. Ni a ganina, ya kamata gwamnati ta samu wasu ’yan kasuwa masu gaskiya da rikon amana ta ba su dama su shigo da shinkafar kuma ta gaya masu yadda take son a sayar. Kuma mu tashi mu noma tamu shinkafar, idan muka noma muka wadata sai a rufe kan iyaka a hana shigo da ita.”
Datse iyakokin ya dace ta wani bangaren – Tasi’u Bako
Hussaini Isah, Jos
Alhaji Tasi’u Bako Nabawa: ‘’Ta wani gefen zamu iya cewa ya dace gwamnati ta ci gaba da rufe kan iyakar kasar nan, don hana shigowa da shinkafa. Domin daukar wannan mataki ya kawo darajar amfani gona a kasar nan, wanda hakan ya karfafa wa manoma gwiwa kan harkokin noma a kasar nan. Wahalhalun da manoma suka shiga a baya, yanzu duk sun kau. Haka kuma idan muka dauki daya bangaren, bai dace gwamnati ta ci gaba da rufe kan iyakar kasar nan don shigowa da shinkafa ba. Musamman idan muka dubi mawuyacin halin da muke ciki a kasar nan na rashin abinci. Don haka ya kamata gwamnati ta busa ta ciza kan wannan mataki da ta dauka.”
Bai kamata a bude iyakokin ba – Rabi’u Yunusa
Musa Kutama, a Kalaba
Alhaji Rabi’u Yunusa: “Gaskiya a wannan marra da ake ciki bai kamata ba a bude boda. Dalilina shi ne, saboda bude ta ba shigo da shinkafar ce kadai ba, ana fakewa ana shigo da makamai da kuma muggan kwayoyi ta kan iyakar, duk dabarar gwamnati mutum ya fi ka dabara. Za a rika fakewa da shigo da shinkafa ana shigo da makamai. Ni ban goyi bayan a bude boda ba.”
Ya dace a
bude iyakokin – Yusuf Ibrahim
Musa Kutama, a Kalaba
Alhaji Yusuf Ibrahim Caba Rawayya: “Gaskiya saboda halin da ake ciki, ya dace a bude boda domin talaka da sauran masu karamin karfi na cikin matsi saboda mutane su samu sauki. Matsala ta halin rayuwa yau da aka tsinci kai a kasar nan, na san na zuwa wani dan lokaci ne amma bude iyakar alheri ce domin a shigo da abinci domin ya wadace mu.”