Ko ya dace a hana sayar da naman daji saboda tsoron yaduwar cutar Ebola?
A yayin da cutar Ebola take ci gaba da hallaka mutane a kasashen da ta bulla a yankin yammacin Afirka, wanda ya sa hukumomi daukar matakan kiyaye bazuwar annobar. Kasancewa daya daga cikin hanyoyin kamuwa da kwayar cutar shi ne cin naman dabbobin daji kamar biri da jemage da gada da sauransu. Abin tambaya a […]
A yayin da cutar Ebola take ci gaba da hallaka mutane a kasashen da ta bulla a yankin yammacin Afirka, wanda ya sa hukumomi daukar matakan kiyaye bazuwar annobar. Kasancewa daya daga cikin hanyoyin kamuwa da kwayar cutar shi ne cin naman dabbobin daji kamar biri da jemage da gada da sauransu. Abin tambaya a nan shi ne, shin ya dace a hana sayar da naman daji saboda tsoron yaduwar cutar Ebola?
Bai dace a hana ba-Mohammed Garba
Mohammed Garba: “A ganina bai dace a bari ana sayar da naman daji ba har sai an samu maganin wannan cutar. Saboda yadda wannan annobar take saurin kisa da bazuwa, ya dace ne a haramta cin har sai bayan an shawo kanta. Musamman ma ganin cewa wannan naman da ake magana akai bashi ne kadai nama ba, kuma akwai sauran dabbobin gida da za a iya ci ba tare mutum ya sa kansa a fargabar kamuwa da kwayar cutar ba.”