Ko ya dace a hana sayar da naman daji saboda tsoron yaduwar cutar Ebola? 1

A yayin da cutar Ebola take ci gaba da hallaka mutane a kasashen da ta bulla a yankin yammacin Afirka, wanda ya sa hukumomi daukar matakan kiyaye bazuwar annobar. Kasancewa  daya daga cikin hanyoyin kamuwa da kwayar cutar shi ne cin naman dabbobin daji kamar biri da jemage da gada da sauransu. Abin tambaya a […]

Ko ya dace a hana sayar da naman daji saboda tsoron yaduwar cutar Ebola? 1
Ko ya dace a hana sayar da naman daji saboda tsoron yaduwar cutar Ebola? 1

A yayin da cutar Ebola take ci gaba da hallaka mutane a kasashen da ta bulla a yankin yammacin Afirka, wanda ya sa hukumomi daukar matakan kiyaye bazuwar annobar. Kasancewa  daya daga cikin hanyoyin kamuwa da kwayar cutar shi ne cin naman dabbobin daji kamar biri da jemage da gada da sauransu. Abin tambaya a nan shi ne, shin ya dace a hana sayar da naman daji saboda tsoron yaduwar cutar Ebola?

Yakamata a hana- Jingudo Muhammed                                      

Jingudo Muhammad: “A gaskiya  bai dace ba ace gwamnatin kasar nan ta  bari masu sayar da naman dabbobin daji da wanda benciken masana ya tabbatar da cewa naman da suke sayardawa yana dauke da kwayar cutar Ebola. Saboda  idan aka bari aka ci gaba da sayar da irin wannan naman ga jama’a tamkar an taimaka ne wajen yaduwar wannan cutar ke nan .Don haka muddin da gaske ake son a kawar da wannan cutar a cikin kankanin lokaci da ake bukata, to wajibi ne sai an dakile yaduwarta.  Bugu da kari ya dace gwamnati ta hana shugo da duk wani naman wata dabbar da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta tabbbatar cin namanta yana cutarwa ga lafiyar jama’a domin lafiyar alumman kasa ya fi komai  muhimmanci, Alla ya karemu.”