Ko ya dace a hana sayar da naman daji saboda tsoron yaduwar cutar Ebola? 2
A yayin da cutar Ebola take ci gaba da hallaka mutane a kasashen da ta bulla a yankin yammacin Afirka, wanda ya sa hukumomi daukar matakan kiyaye bazuwar annobar. Kasancewa daya daga cikin hanyoyin kamuwa da kwayar cutar shi ne cin naman dabbobin daji kamar biri da jemage da gada da sauransu. Abin tambaya a […]
A yayin da cutar Ebola take ci gaba da hallaka mutane a kasashen da ta bulla a yankin yammacin Afirka, wanda ya sa hukumomi daukar matakan kiyaye bazuwar annobar. Kasancewa daya daga cikin hanyoyin kamuwa da kwayar cutar shi ne cin naman dabbobin daji kamar biri da jemage da gada da sauransu. Abin tambaya a nan shi ne, shin ya dace a hana sayar da naman daji saboda tsoron yaduwar cutar Ebola?
Bai kamata a hana ba -Mohammed Khamisu Yakubu
Mohammed Khamisu Yakubu: “Me ye yake cikin naman daji har da za a rika tsoron cinsa, ko kasuwancinsa. Wanda duk ke wannan maganar bai yadda cewa ALLAH ne ke kawo ciwo ba kuma shi ke samar da waraka ba. Ka gat un da wannan annobar ta kunno kai hatta mu masu sana’ar sayar da gasasshen nama hakan na shafar su. Kuma ai ba duka naman daji ke haifar da cutar Ebola ba, an bayyana wasu dabbobi ne da ba su wuce biyu ko uku ba, ka ga me ne dalilin cewa a hana sayar da naman daji.”