Ko ya dace a hana sayar da naman daji saboda tsoron yaduwar cutar Ebola? 3
A yayin da cutar Ebola take ci gaba da hallaka mutane a kasashen da ta bulla a yankin yammacin Afirka, wanda ya sa hukumomi daukar matakan kiyaye bazuwar annobar. Kasancewa daya daga cikin hanyoyin kamuwa da kwayar cutar shi ne cin naman dabbobin daji kamar biri da jemage da gada da sauransu. Abin tambaya a […]
A yayin da cutar Ebola take ci gaba da hallaka mutane a kasashen da ta bulla a yankin yammacin Afirka, wanda ya sa hukumomi daukar matakan kiyaye bazuwar annobar. Kasancewa daya daga cikin hanyoyin kamuwa da kwayar cutar shi ne cin naman dabbobin daji kamar biri da jemage da gada da sauransu. Abin tambaya a nan shi ne, shin ya dace a hana sayar da naman daji saboda tsoron yaduwar cutar Ebola?
Ya dace a hana- Lawal Muhammad Inuwa
Lawal Muhammed Inuwa: “Batun gaskiya ina ganin ya kamata a ce gwamnatin kasannan ta dauki matakin hana sayar da naman duk wata dabba da binciken masana suka tabbatar da illarta ga lafiyar jama’a musamman kamar irin birrai da gemagu da beraye da sauransu wadanda masana kiwon lafiya suka tabbatar da lallai suna yada kwayoyin cuta ciki har da cutar Ebola. Saboda ko a shekarun baya ai Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO)ta taba bayyana ce wa asalin cutar nan mai karya garkuwar jiki wato kanjamau daga birrai ne aka sameta da kuma karnuka. Kuma ya kamata a ce jama’a su bi shawarwarin hukumar WHO domin samun kariya da kawar da wannan annobar.