Ko ya dace a hana sayar da naman daji saboda tsoron yaduwar cutar Ebola? 4
A yayin da cutar Ebola take ci gaba da hallaka mutane a kasashen da ta bulla a yankin yammacin Afirka, wanda ya sa hukumomi daukar matakan kiyaye bazuwar annobar. Kasancewa daya daga cikin hanyoyin kamuwa da kwayar cutar shi ne cin naman dabbobin daji kamar biri da jemage da gada da sauransu. Abin tambaya a […]
A yayin da cutar Ebola take ci gaba da hallaka mutane a kasashen da ta bulla a yankin yammacin Afirka, wanda ya sa hukumomi daukar matakan kiyaye bazuwar annobar. Kasancewa daya daga cikin hanyoyin kamuwa da kwayar cutar shi ne cin naman dabbobin daji kamar biri da jemage da gada da sauransu. Abin tambaya a nan shi ne, shin ya dace a hana sayar da naman daji saboda tsoron yaduwar cutar Ebola?
daukar matakin zai taimaka- Ibrahim Adamu
Ibrahim Adamu: “A gaskiya ya kamata hukumoni su dauki matakan da za su kawo karshen bazuwar cutar Ebola saboda wannan ne ya sa nake goyon bayan duk wani mataki don kawo karshen yaduwar annobar. Musamman ma idan aka yi la’akari da yadda wannan cutar take da saurin kisa da bazuwa cikin kankanin lokaci.”