Ko ya dace a kafa hukuma da kotunan kula da sakin aure a Najeriya?

A yayin gudanar taron tattauna al’amuran kasa, Sanata dansadau ya bayar da shawarar cewa ya dace a kafa hukuma da kotuna masu zaman kansu, wadanda za su kula da al’amuran sakin aure a kasar nan. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a yi haka? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga […]

Ko ya dace a kafa hukuma da kotunan kula da sakin aure a Najeriya?
Ko ya dace a kafa hukuma da kotunan kula da sakin aure a Najeriya?

A yayin gudanar taron tattauna al’amuran kasa, Sanata dansadau ya bayar da shawarar cewa ya dace a kafa hukuma da kotuna masu zaman kansu, wadanda za su kula da al’amuran sakin aure a kasar nan. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a yi haka? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa:

Ya dace a kafa hukumar  – Sheikh Hussaini

Sheikh Hussaini Zakariyya: “Kafa hukumar ya dace matukar za ta yi amfani da tanadin addini saboda sakin aure na da sharudda da ladubba, kamar yadda daura shi ke da shi. Mutum bai auran mace haka nan har sai ya je wajen danginta, ya je wajen iyayenta, an yi gaisuwa da bincike, ya kuma bayar sannan a yi aure. To haka lamarin yake wajen sakinsa, sai an bi dukkan matakai idan har lamarin ya ci tura, to shi ke nan. Malamai na cewa babban abin da Allah ke fushi da shi daga cikin abin da Ya halatta shi ne sakin aure.”